Connect with us

KIWON LAFIYA

WHO Ta Bayyana Kawo karshen Annobar Ebola Karo Na Goma

Published

on

Ranar Alhamis ta makon daya gabata ne Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana karshen barkewar annobar cutar Ebola karo na goma, bayan gumurzun da aka yi tayi na shekarau biyu da suka wuce a kasar jamhuriyyar damukuradiyyar kasar Kongo.

Darektan ofishin Afirka wanda a kasar Kongo Brazzabille, shi ne wanda ya bayyana hakan, a kafar sadarwar sa ta twitter @WHOAFRO.

Ya ci gaba da bayanin cewar “Yau barkewar cutar Ebola karo na goma ta kawo karshe a jamhuriyyar damukuradiyyar kasar Kongo.

Da ya ke kara haske dangane da shi al’amarin cewa yayi “Muna iya tunawa da fafutukar ko kuma gwagwarmayar da muka faro shekaru biyu da suka gabata, wajen kokarin mu na cewar sai, mun ga karshen wannan cutar, yau ga shi mun  shi burin’’.

A sanarwar data fitar ta kafar sadarwar ta yanar gizo Hukumar wadda take karkashin majalisar dinkin duniya, ta bayyana cewar, ma’aikatar lafiya ta kasar jamhuriyyar damukuradiyyar kasar Congota bayyana cewar ba a samu wanda ya kamu da cutar ba kawanki 42, bayan da aka samu mutum na karshe wanda aka gwada aka samu bai kamu da cutar ba.

“ Ita dai  a watan Agusta na shekararwannan annoba ta fara barkewa ne 2018, inda aka samu mutane 3,470 cases wadanda suka kamu da cutar, daga cikin su kuma mutum 2,287 sun rasa rayukan su, ya yin da kuma mutane 1,171 suka warke. Wancan lokacin ne aka samu mummunar barkwar ita cutar ta Ebola, bayan wadda ta bayyana a yammacin Afirka a shekarun 2014 da kuma 2016.

“A cikin wani yanayi na tabarbarewar tsaro duk wani kokarin da aka yi na hana yaduwar cutar Ebola karo na goma a kasar ta Congo abin da akwai matsalolin masu matukar wuya.

“Tawagar kawo daukin gaggawa daga Ita Hukumar lafiya ta duniya sai kuma kungiyoyi da su ke abokan tafiya kamar ma’aikatar lafiya ta kasar Congo da kuma al’umma hakika sun bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen ganin an kawo karshen ita annobar.’’

Ita dai wannan sanarwar ta fito ne daga bakin babban jami’i wanda kuma shi ne shugaban sashen gabashin Afirka Dokta Matshidiso Moeti shi ne wanda ya bayyana cewar“Lokacin da aka share shekaru biyu ana kokarin yadda za a kawo karshen barkewar ita cutar Ebola Hukumar lafiya ta duniya tare da kawayenta sun kara karfafawa su Hukumomin lafiya na gida akan yadda za su yi maganin ita annobar.

Bugu da kari kamar dai yadda ya yi karin haske inda kuma ya ce “yanzu ita jamhuriyyar damukuradiyyar kasar ta Congo shirye ta ke ko wanne lokaci akan abinda ka iya tasowa na bangaren kula da lafiyar fiye da yadda aka santa, wannan kuma fa abin da ake sa ran cewar zai dore ne, kamar dai yadda ake tunkarar barkewar cutar Cbid -19.”

Hukumar lafiyata duniya ta bayyana cewar darussan da aka koya ana yin mafani dasu ta bangarorin al’amuran gaggawa na la kula da lafiyar al’umma.

“Yawancin abubuwan da aka yi amfani dasu wajen tunkarar ita cutar Ebola, wadanda suka hada da yadda za a gano wanda ko kuma wadanda suka kamu da ita cutar, hana yaduwar ita cutar, sai kuma killace wadanda suka kamu da cutar. Sai kuma wadanda ake tsammanin sun kamu da cutar. Haka ne ake yi wannan lokacin na annobar cutar Coronabirus ko kuma abin da aka fi sani da CObID-19, a kasar inda aka samu fiye da mutane 6,000 da aka tabbatar da cewar sun kamu.

“Hukumar lafiya tana taimakawa kasashen nahiyar Afirka lokacin da cutar CObID-19 ta kasance wani al’amari mai ban takaici, wannan ya hada da samar masu da kayayyaki da kuma kwararru wajen kawo dauki.

“Bugu da kari kuma ita Hukumar tana taimakawa kasashe wajen yadda za su iya tafiyar da harkokin lafiya wadanda suka kasance dole ne sai an yi su, sai kuma duk yadda za su yi a cigaba da kula da lafiyar al’umma kamar yadda aka saba. Ga kuma yadda aka samu damar sassauta hana fita saboda kare mutane daga kamuwa da cututtukan da za a iya shawo kansu ta hanyar magani kamar dai zazzabin cizon sauro kamar dai yadda ya bayyana”.

Halin da ake ciki yanzu shugaban Hukumar lafiya ta duniua Tedros Ghebreyesus ya bayyana cewar ana mai alfahari da yi aiki tare da gwamnatin kasar jamhuriyyar damukuradiyya ta Congo, wajen ganin an ga karshen annobar cutar Ebola.

“Wannan kamar dai yadda ya yi karin haske cewar an samu cimma ita nasarar ce da taimakon ayyukan sadaukarwa na dubban ma’aikatan lafaiya na kasar ta Congo, wadanda suka yi aiki kafada- kafada da tkwarorinsu na Hukumar lafiya ta duniya. Sai kuma sauran abokan tafiya na ita Hukumar kowa dai ya dace kuma a jinjina maku.

“Yawancin matakan da aka dauka an samu sa’ar cimma burin yin amfani dasu, musamman ma wajen kawo karshen ita cutar Ebola, har ila yau dai irin matakan ne aka dauka wajen tunkarar ita cutar ta CObID-19:

“Maganar yadda za a iya gano ko an kamu da duk wata cuta da kuma ware wadanda suka kamu, yadda ake gwajin ko wacce matsala, ga kuma yadda za a kula ga kuma maganar yadda za a gano wadanda suka kamu da cutar. Wadannn sune matakan da suka kasance kashin bayan duk wata nasarar da aka samu ta yadda za a tunkari cuta a ko wacce, daga nan kuma ba wani siddabarun da zai iya yiyuwa

“Sai dai kuma wani al’amari mai wuya da tayar da hankali shi ne cututtukan Ebola da kuma  CObID-19  sune cututtuka biyu da su ke samar da babban kalubale ga al’ummar kasar Congo, sai kuma sauran kasashen ‘yan tsaka-tsaki ne da kuma ‘yan rabbana ka wadata mu.

“Wannan ma shi yasa ita Hukumar lafiya tac duniya ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta ci gaba da yin aiki da al’umma da kuma gwamnatin kasar Congo, domin a samu kara bunkasa sashen kula da lafiyar al’umma, har ma samu kaiwa a irin mizanin kula da lafiyar al’umma, kamar dai yadda dokokin kasa da kasa suka fayyace a cikin jawabinsa kamar yadda dai shi shugaban Hukumar lafiya ta duniya Mista Ghebreyesus ya bayyana.”

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: