Bello Hamza" />

WHO Ta Bukaci Yara Daga Shekara 11 Su Fara Sa Takunkumin Fuska Don Kariya Daga Cutar Korona

Gidauniyar yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta ce, ya kamata yara da suka zarce shekara 11 su lizimci sanya takunkumin fuska in sun samu kansu a cikin taron jama’a a matsayin mataki na kariya daga cutar korona.

Hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya WHO ta sanar da haka a takardar sanarwa da ta raba wa manema labarai ranar Juma’a da yamma.

WHO da UNICEF ba su tilasta wa yara masu shekara 6 zuwa 11 cewa dole su sanya takunkumi ba amma ana iya sawa a inda ake zargin za a iya kamuwa da cutar kamar makaranta da saura wajen cunkoso.

Amma lallai akwai wuraren da takunkumin zai iya haifar da cikas ga harkar daukar karatu a saboda haka ya kamata a kula don kada kilu ya jawo bau.

Exit mobile version