Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta jinjinawa kwazon kasar Sin, na gabatar da alkaluman rigakafin cutar COVID-19 domin yin nazarin su.
WHO dai na fatan auna ingancin nau’o’in rigakafin ta kasar Sin, don tabbatar da ingancita a fannin bukatar gaggawa, kamar dai yadda Katherine O’Brien, babbar jami’a a hukumar ta WHO ta bayyana a jiya Talata.
O’Brien ta ce yanzu haka akwai nau’o’i biyu na rigakafin Sin, na kamfanin Sinopharm da Sinovac da WHO ke yin gwajin ingancin su.
Jami’ar wadda ita ce darakta mai lura da sashen rigakafi da dangoginsa a WHO, ta ce an riga an tattarawa hukumar alkaluman da suka shafi rigakafin, sai dai kwararrun da za su yi aikin, na jiran kammala wa’adin killacewa, kafin halartar wuraren da ake sarrafa rigakafin don yin nazarin su. (Saminu Hassan)