WHO Ta Kira Taron Gaggawa Kan Sabbin Nau’ikan Korona

WHO

Kwamitin kar ta kwana na hukumar lafiya ta duniya (WHO), ya kira wani taron gaggawa da ya tattauna matakan dakile barazanar da duniya ke fuskanta na sabbin nau’ikan cutar Korona da a yanzu ke yaduwa cikin gaggawa.

Yaduwar sabbin nau’ikan cutar ta Korona na cigaba da yin karfi a tsakanin kasashe a daidai lokacin da hukumomi suka sake kakaba dokokin takaita walwala ciki har da kulle yankuna da dama, sakamakon sake barkewar da annobar ta yi a zango na biyu.

Batutuwa masu alaka da yaduwar sabbin nau’ikan cutar, aiwatar da shirin yiwa jama’a alluran rigakafi da kuma tsaurara yiwa matafiya gwajin cutar ne suka mamaye taron na WHO da ya gudana shekaran jiya Alhamis a Geneba.

WHO ta bayyana fargaba kan halin da Duniya ta tsinci kanta duk da matakin ci gaba da yiwa jama’a alluran rigakafin cutar ta Korona cutar da zuwa yanzu ta hallaka mutane miliyan 1 da dubu 954 da 336 tun bayan barkewarta cikin watan Disamban 2019 a yankin Wuhan na tsakiyar China.

Masana dai na fargaba kan mai yiwuwa sabbin nau’ikan cutar ta Korona su bijirewa alluran rigakafin da aka samar a baya bayan nan, wadanda kawo yanzu shugaban ayyukan gaggawa na WHO Michael Ryan ke cewa sun raba adadin da ya kai miliyan 28 a tsakanin kasashe 46.

Cikin rahotonta na mako mako, WHO ta ce sabuwar nau’in cutar da ta fara bulla a Birtaniya ta yadu zuwa kasashe 50, yayinda nau’in wadda aka gano a Afrika ta kudu kuma ta yadu a kasashe 20.

Exit mobile version