Bello Hamza" />

WHO Ta Samar Da Tallafi Ga Kasashen Da Suka Fi Kamuwa Da Cutar Korona A Afrika

Tawagar farko na kwararu daga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta isa kasar Afrika ta Kudu don kai tallfi na musamman akan annobar cutar korona, haka na daga cikin tallafin da hukumar ta shirya don ba kasashen Afrika ta suka fi kamuwa da cutar korona.

Hukmar Lafiyar ta WHO ta bayyana haka ne a shafinta na tiwita daga ofishinta dake kasar Kongo.

Sanarwa ta kuma kara da cewa, a yayin da yawan masu cutar a Afrika ya dunkari mutum Miliyan daya, hukumar ta kara karkatar da kokarin tallafinta ne ga kasashen da cutar ta fi kamari, musamman ganin yawan masu cutar a Afrika ya kai mutum Miliyan daya.

“Kasar Afrika ta Kudu ne ke kan gaba a Afrika na masu cutar, kuma da jami’an mu da suka isa kasar sai da suka killace kansu kamar yadda dokokin kasar ya tanada.

“Masana da suka kai mutum 40 ana sa ran za su yi aiki tare da likitocin kasar ne na karfafa yadda ake fuskantar cutar a kasar.’’

Sanarwa wadda shugaban yanki na hukumar, Dr Matshidiso Moeti, ya sanya wa hannu ya ce, dole a sanya ido a kasashen da cutar ta fi kamari don dakile yaduwar a tsakanin al’umma.

Exit mobile version