Connect with us

KIWON LAFIYA

WHO Ta Shawarci Kasashe Su Kara Harajin Sigari

Published

on

Ranar 31 ga watan Mayu na duk shekara ce hukumar kiwon lafiya ta dunya ta ware a matsayin ranar wayar da kai akn illolin dake tattare da shan sigari.

A bikin na shekarar 2018 da aka gudanar a kwanan baya a daukacin fadin duniya WHO ta yi amfani da ranar inda ya yi kira ga daukacin kasashen duniya su kara harajin da suke karba akan sigari don a rage sayen ta.

Wannan shawarar tana kunshe ne a cikin sakon da hukumar ta fitar don tunawa da zagayowar ranar.

WHO ta kuma shawarci kasashen dasu tsawwala akan tallace-tallacen da ake yi da daukar nauyi da kuma sanya ido akan yadda ake yin ta’ammali da sigari a kasashen su.

Taken taron na bana shine “Sigari da cututtukan zuciya dake janyowa.”

Hukumar ta nuna damuwar ta akan yadda masu ta’amalli da sigari suke mutuwa sakamakon kamuwa da cituttuka, inda ta ce, kimanin masu ta’amalli da ita miliyan bakwai ne suka mutuwa a duk shekara.

WHO ta kuma yi kira ga kasashen dasu kare alummamomin su wajen shakar hayakin na sigari a cikin gari da wuraren aiki da kuma a cikin motocin haya.

WHO ta kuma shawarci kasashen dasu taimakawa masu ta’amalli da sigari da suka son daina yin dabi’ar  ta wajen daukar nauyin maganin cutututtukan da suka kamu dasu saboda ta’ammali da sigarin.

Hukumar kuma yi kira ga gwamnatocin dasu dauki matakai wajen rage yin amfani da sigarin don kare masu ta’ammali da ita wajen kamuwa da cututtuka.

Hukumar ta yi nuni da cewa, kimanin kashi tamanin sama da mutane biliyan daya a duniya masu ta’amalli da sigari suna zaune a kasashe masu karamin tattalin arzikin kasan inda masu ta’amallin da suka kamu suke saurin mutuwa..

WHO ta yi nuni da cewar cutar CBD tafi kashe mutane fiye da sauran cututtuka a fadin duniya, inda kuma masu shakar hayakin wadanda suka kai kashi sha biyu suna kamuwa da cututtukan zuciya da ka iya zama ajalin su.

A cewar hukumar, yin ta’ammali da sigaro itace ta biyu dake janyo hawan jini, inda ta shawarci kasashen duniya dasu zage wajen wayar da kan alummar su akan illolin dake tattare da yin ta’ammali da sigari.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: