Muhammad Mait" />

WHO Ta Tallafa Wa Ma’aikatan Lafiya 5,500 A Yankin Arewa Maso Gabas

Kungiyar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana yadda ta tallafa wa ma’aikatan kiwon lafiya kimanin 5,500, ta hanyar basu horo tare da samun kwarewa a fagen aikin kiwon lafiya, a yankunan da matsalar tsaro ta shafa a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

Kungiyar kula da lafiya ta duniya ta shaidar da cewa, wannan tallafi wanda ta bai wa ma’aikatan kiwon lafiya, sun kunshi basu horo da dabarun yadda zasu fuskanci yanayin da matsalar tsaro ta samar a sha’anin kiwon lafiya da gagarumar rawar da ya dace su taka a yankin arewa maso gabas.

Wadannan suna kunshe ne a cikin wani rahoton da kungiyar WHO ke fitarwa a kowane mako, a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

“Bisa yadda ake da bukatu da kwarewa a tsarin kiwon lafiya a wannan yanki na arewa maso gabas, akwai bukatar zare dantse da azama wajen kokarin ceto rayukan jama’a masu dimbin yawa a fannin kiwon lafiya, a wuraren da lamarin ya shafa”. Kamar yadda rahoton ya nuna.

Bugu da kari kuma, rahoton ya bayar da alkaluma na kimanin mutane miliyan 5.3, da suka hada da kananan yara miliyan hudu, wadanda ke bukatar kula da lafiyar su a cikin gaggawa a yankin.

A hannu guda kuma, kngiyar WHO ta yi imani kan cewa, samar da tallafi ta hanyar horo da kwarewa, shi ne babban jigon matakin da zai kai tsarin inganta kiwon lafiya cikin hanzari.

Da ya ke ta’aliki dangane da lamarin, babban jami’in kungiyar WHO a Nijeriya; Dr. Clement Lasuba, bayyana cewa ya yi, “Ta hanyar bayar da tallafin bunkasa ilimi da kwarewar, su na daga cikin manufofin WHO, wanda amfanin su bai tsaya kawai wajen bunkasa kwarewar ma’aikatan kiwon lafiya ba, kuma zai taimaka wajen ceto dimbin rayukan jama’a.”

Exit mobile version