Abubakar Abba" />

WHO Ta Yi Gargadin Kada Ayi Saurin Murnar Kakkabe Ebola A Kongo

Shugaban hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Ghebreyesus ya sanar da cewar ya yi gargadi akan saurin cewar anci nasara akan yakar cutar Ebola a kasar jamhuriyar Kongo, duk da cewar, akwai alamomin dake nuna cewar kilan an shawo kancutar.

Tedros Ghebreyesus ya shedawa manema labarai hakan ne  a lokacin da ya kai ziyara a Kinshasa  babban birnin kasar  ta Kongo.

Yi nuni da cewar, koda yake, barkewar cutar tana raguwa amma duk da haka yaduwar bata kare ba.

Shugaban ya kara da cewa,“har yanzu muna kan yakin kuma muna bukatar mu ci gaba da karfafa sanya ido.”

A ranar juma’ar data gabata ce jami’an hukumar suka sanar da cewar, annobar tana sauka ganin yadda aka tura magungunan yakar cutar.

Amma bayan kwana daya, ma’aikatar kiwon ta kasa ta tabbatar da bullar annobar a karon farko a satin da ya gabata a wani yanki dake Iboko.

Mista Ghebreyesus ya bayyana cewar, kimanin mutane 2,200 aka yi masu allurar rigakafbin cutar da kuma gano wadanda suka kamu da cutar.

Sai dai Mista Ghebreyesus ya bayyana cewar, har yanzu annobar bata riga ta tafi baki daya ba, inda ya yi nuni da cewar, koda kyayar cutar daya ce ta tsallaka cikin Kongo har ta kai wani yankin kasar, zata iya kara habakar yauwar annobar.

Tun lokacin sabuwar cutar ta bulla a kasar a cikin watan Afirilu, kimanin mutane ashirin da bakwai ne suka sheka lahira an kuma samu bullar cutar guda sittin da biyu, inda aka tabbatar da guda talatin da biyu a dakin gwajin  cututtuka.

Ana kuma kirdadon annabar guda sha hudun, inda kuma karin wasu mutane goma da ake zargin suma sun kamu da cutar.

Sabanin a baya barkewar cutar, ma’aikatan kiwon lafiya a yanzu suna yin hanzarin dakile yadduwar cutar a kasar ta Kongo.

Annobar ta dai hallaka a kalla mutane 11,300 daga shekarar 2013 zuwa shekarar 2016 a yammacin Afrika,inda aka a wancan lokacin barkewar aka soki hukumar (WHO) akan sakacin wajen daukar matakin gaggawa tun a matakin farko.

A ranar 14 ga watan Mayu, kafar dillancin labarai ta kasa, ta ruwaito cewar  WHO ta baiwa jami’an ta dake kasar Kongo umarnin dasu shigo da magungunan  Ebola da aka yi gwajin su a cikin kasar.

Magungunan da Merck ya sarrafa su a shekarar 2016, an tabbatar suna da inganci ga alumma duk da cewar ba’a baiwa maganin lasisi ba.

Ana iya ajiye shi  akan ma’auni yanayi kashi 60 zuwa 80 na Celsius, inda hakan yake kirkiro da manyan kalubale.

Wanda kuma aka yi gwajin sa a kasar Guinea a shekarar  2015 a tun farko lokacin da annobar ta kazanta Afrika ta yamma, an tsara shi ne don yin amfani dashi a wajen yin allurar rigakafin jeka nayi ka.

Ma’ana a nan, a lokacin da aka yi gwajin  sabuwar annobar, dukkan mutanen da ake tunanin sun kamu da cutar a baya, an gano su aka kuma yi masu rigakafin cutar don dakile yaduwar ta.

 

Exit mobile version