Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

WHO: Tabbas Ne Cutar COVID-19 Ta Bullo Daga Indallahi

Published

on

A yayin wani taron manema labaru da WHO ta saba shiryawa a jiya Juma’a a Geneva, game da shakkar ko cutar COVID-19 ta fito daga cibiyar nazarin kwayoyin cututtuka ta Wuhan? Jami’in hukumar mai kula da haliln ko ta kwana Michael Ryan ya ce, akwai dimbin shaidu da masu nazarin kimiyya da dama suka samu sun tabbatar cewa, wannan cuta na samun asali ne daga indallahi.

Kazalika darakta janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya mai da martani dangane da zargin da aka yi wa hukumar na gazawa wajen ayyana cutar COVID-19 a matsayin matsalar kiwon lafiya dake bukatar daukin gaggawa daga kasa da kasa a kan lokaci, inda ya ce, WHO ta yi gargadi kan lokaci, matakin da ya baiwa duk duniya isashen lokacin tinkarar cutar. Ya ce a ranar 30 ga watan Jarairu, kwamitin hukumar ya cimma matsayar sanar da cutar a matsayin matsalar lafiya dake bukatar daukin gaggawa, kuma a waccan lokaci mutane 82 ne kadai suka kamu da ita a duniya, ban da a kasar Sin, kuma babu wanda ya rasa ransa sakamakon cutar, abin da ya bayyana cewa, akwai isashen lokacin yin kandagarkin cutar.
Bugu da kari, hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi maraba da labarin dake cewa, babu wani mai dauke da cutar COVID-19 dake kwance a asibitin birnin Wuhan na kasar Sin, inda ta jinjinawa namijin kokarin da kasar Sin ta yi wajen dakile annobar.
Bayan shafe sama da watanni 3 ana yaki da cutar, yanzu a birnin Wuhan dake yankin tsakiyar kasar Sin, da ya taba kasancewa inda cutar COVID-19 ta fi kamari, an sallami dukkan wadanda suka kamu da cutar COVID-19 dake kwance a asibiti, bayan sun warke, a ranar Lahadin da ta gabata.
Yayin wani taro ta kafar bidiyo, shugabar shirin ayyukan lafiya na gaggawa na WHO, Maria Van Kerkhove, ta ce abun farin ciki ne jin cewa babu wani dake cikin yanayi mai tsanani ko yake dauke da cutar a birnin Wuhan.
Maria Kerkhove, wadda ke cikin tawagar kwararru na hadin gwiwa tsakanin Sin da WHO da suka ziyarci kasar Sin a watan Fabreru domin nazartar yanayin da ake ciki, ta ce kasar Sin ta yi namijin kokari wajen dakile yaduwar cutar. (Fa’iza Mustapha)
Advertisement

labarai