Ana sa ran gwamnatin Thailand za ta sayi alluran riga-kafin COVID-19 miliyan biyu wanda kamfanin hada magunguna na kasar Sinovac Biotech ya samar, ofishin hukumar lafiya ta duniya ta WHO dake Thailand ya sanar da hakan a ranar Lahadi.
Hukumar lafiyar kasar Thailand MOPH, tana tsammanin karbar kashin farko na alluran kimanin 200,000 wanda ake sa ran za su isa kasar nan da karshen watan Fabrairu, kashi na biyu na alluran 800,000 za su isa kasar zuwa karshen watan Maris, yayin da ragowar alluran riga-kafin miliyan daya za su isa kasar a karshen watan Afrilu, a cewar rahoton hukumar ta WHO.
An samu rahoton barkewar annobar COVID-19 na baya bayan nan a Thailand, a yankin Samut Sakhon, a wani lardin gabar teku dake daura da babban birnin kasar Bangkok, daga bisani annobar ta yadu zuwa sama da kashi biyu bisa uku na dukkan larduna da yankunan kasar. Jimillar adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar Thailand ya kai 7,694 ya zuwa ranar Lahadi daga kasa da mutane 4,300 a tsakiyar watan Disamba. (Mai Fassarawa: Ahmad Inuwa Fagam)