Muhammad Maitela" />

WHO: ’Yan Gudun Hijira 650,000 Za Su Haukace

Hukumar Kula da Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO) ta bakin babban jami’in ayyukan gaggawa, Dr. Collins Owili, ya bayyana cewa, kimanin mutum miliyan 24.5 ne ke fuskantar matsalolin tabin kwakwalwa a Nijeriya, inda kuma ya nuna cewa, a cikin wadannan alkaluman, kimanin ’yan gudun hijira 650,000 ne za su fuskanci barazanar cutar tabin kwakwalwar, wacce ke nema ta zama ruwan dare.

Ya ce, hakan ya samo asali ne ta dalilin matsalar tsaron Boko Haram da makamantanta, wacce ta shafi Jihohin Borno, Adamawa da Yobe; inda kuma ta jawo asarar rayukan jama’a sama da 37,000 tare da asarar dukiya akalla Dalar Amurika biliyan Tara, wato kimanin Naira tiriliyan 3.42 kenan.

Mista Owili na kungiyar WHO ya bayyana hakan a wata sanarwar manema labarai sakamakon rahotonta na 2016 zuwa 2019 a ranar Lahadin da ta gabata a birnin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Ya kara da cewa, wannan matsala ta tabin kwakwalwa ta na nema ta zama ruwan dare, ta dalilin matsalar tsaron Boko Haram, a wasu alkaluman da asibitin kula da masu tabin hankali na Gwamnatin Tarayya da ke Maiduguri, wanda ita kadai ce a ke da ita a Arewa maso Gabas.

“Akwai fargaba dangane da yawaitar wannan al’amari a irin wannan yanki, wanda a ke fama da karancin kwararun masana a fannin magance matsalar,” in ji rahoton.

Ta bakin Dr. Owili, ya kara da cewa, yanzu haka kaso 18 cikin dari ne kadai na cibiyoyin kiwon lafiya ke gudanar da ayyukan su a jihar Borno, wadanda ke bayar da kwarya-kwaryar kulawa ga mutanen da su ka tsallake rijiya da baya daga matsalar tsaron.

Rahoton ya yi karin haske kan batun yawaitar masu fama da motsin kwakwalwar da cewa, “kungiyar WHO ta gudanar da wata kikkiga, inda ta gano a cikin kowadane yan gudun hijira 5, mutum daya yana da bukatar samun kula ta gaggawa a matsalar cuta mai alaka da tabin kwakwalwa.

“Haka kuma wannan matsalar a arewa maso gabas- Nijeriya, hauhawar lamarin cutar tabin hankali zai iya ribanya wa, matukar aka ci gaba da fuskantar matsalolin zamantakewa, garkuwa da jama’a da kashe-kashe.”

A gefe guda kuma ya ce, wadannan matsalolon za su kara kawo cikas wajen samun yawaitar matsaloli masu nasaba da tunani da dabi’a tare da zama alakakai nan gaba kadai cikin shekaru masu zuwa, musamman a rayuwar yan gudun hijira da yankunan da a ka ’yanto.

Ya ce kungiyar WHO tana namijin kokari wajen hada gwiwa da hukumar ayyukan jinkai ta kasar Amurika (OFDA) hadi da hukumar bayar da gudumawa ga ayyukan jinkai ta Nijeriya (NHF) hadi da asibitin kula da masu tabin hankali da ke Maiduguri (Neuro -Psychiatric Hospital) domin tsara aikin bunkasa hanyoyin kula da irin wadannan matsalolin.

Exit mobile version