WHO Za Ta Kashe Dala Miliyan 178 Kan Kiwon Lafiya A Nijeriya

Daga Idris Aliyu Daudawa

Ranar Litinin ne Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce zata kashe kudade har dalar Amurka milyan 178 tsakanin shekarun 2018 da kuma 2019, akan al’amuran da suka shafi harkar lafiya a Nijeriya.

Wakili mai kulawa da ofishin Nijeriya na Hukumar lafiya ta duniya Dokta Wondimagegnehu Alemu, shi ne ya bayyana haka lokacin ta aka yi taron hadin guiwa na amincewa da kudaden da za a kashe a kasafin kudi na shekarun 2018 da kuma 2019, tare da Ministan lafiya Farfesa Isaac Adewole a Abuja.

Alemu ya ce, dalar Amurka milyan 127 wadda kashi 66  cikin 100 ne na kasafin kudin, wadanda za a kashe su ne wajen tsare tsaren mganin shan Inna wato polio.

Ya kara da cewar dalar Amurka milyan 30 za a kashe kudaden wajen maganin zazzabin malaria, tarin fuka, da kuma cutare kanjamau.

Ya jaddada cewar dalar Amurka fiye da milyan 8.1 an ware ta ne za akashe wajen kula da lafiya ta hanyar rage mutuwar kananan yara, da kuma tsarin tazarar haihuwa.

Ya yi karin bayani na cewar sauran kudaden za a kashe su ne ta hanyar ta maganar bullar kota kwana, wato annoba ta cututtuka.

Wakilin Hukumar wanda ya bayyana ya sa hannu a kasafin kudina madadin Darektan, ya bayyana cear shi Darektan ya amince da kasafin kudin.

Bugu da kari za arika yin taron tuntuba tsakanin masu ruwa da tsaki, domin a tabbatar da ana yin al’amuran kasafin kudin kamar yadada aka amince.

A nashi jawabin Adewole  ya jinjinawa Hukumar lafiya ta duniya, a kokarin data ke yi na bunkasa harkokin kiwon lafiya a Nijeriya.

Ya bayyana Nijeriya ta samu gudunmawa mai yawa da ga Hukumar,don haka sa hannu a kasafin kudin wani abu ne da ke nuna cewar Hukumar zata ci gaba da taimkawa Nijeriya.

Shi ma Ministan lafiya ya jinjinawa ita Hukumar lafiya ta duniya, sabioda taimakon da take ba Nijeriya, musamman ma al’amarin da ya shafi kawar da cutar polio.

Maganar kasafin kudi na kawar da kwayar cutar polio babban al’amari ne, don haka za ayi amfani da kudaden kamar yadda aka baiyana.

Ya ce, ‘’Ina farinciki akan kudaden da aka ware ma cututtuka masusaurin yaduwa, saboda yaan kasafin kudin can zai fi amfani.

‘’A madadin al’ummar Nijeriya da kuma gwamnati, ina mai nuna farin ciki na akan gudunmawar da aka bamu, da kuma wadda muka yi ta masa daga Hukumar’’.

Kasashen W

Exit mobile version