Abba Ibrahim Wada" />

Wilfred Zaha: Crystal Palace Ta Yi Fatali Da Tayin Fam Miliyan 40 Daga Arsenal

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace tayi fatali da tayin kudi na fam miliyan 40 wanda Arsenal tayi domin sayan dan wasanta na gaba, Wlfred Zaha, wanda ya nuna karara cewa yanason barin kungiyar ta Crystal Palace.

A ranar Litinin Arsenal ta mika tayin farko na fan miliyan 40 domin sayen dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha kuma babu wani dan wasa da aka hada da shi a tayin, wanda ake sa ran Palace za ta yi watsi da shit un farko.

Dan wasan mai shekara 26 na so ya bar kungiyar kuma ya fi so ya koma Arsenal, amma Palace ta yi wa dan kwallon na Ibory Coast farashin fan miliyan 80 sai dai  Arsenal za ta so gannin an sassauta farashin sannan a amince mata ta biya kudin da kadan-kadan.

Yukurin Arsenal na sayen ‘yan wasa a wannan kaka ya fuskanci nakasu saboda kasa zuwa gasar Zakarun Turai ta badi da ta yi wanda hakan yasa hukumomin kungiyar suka ware fam miliyan 45 kacal domin sayan sababbin ‘yan wasa.

Dan uwan Zaha, Judicael, ya shaida wa manema labarai cewa Ganin irin rawar da dan uwansa Wilfried Zaha ya taka a Crystal Palace, ina fatan Palace za su duba hakan domin cimma yarjejeniya da Arsenal da za ta ba shi damar buga gasar Turai a kungiyar da ya dade yana marawa baya tun yana karamin yaro.

Crystal Palace dai tayiwa dan wasa Zaha kudi fam miliyan 100 ga duk kungiyar da takeson sayansa sai dai abune mai wahala Arsenal ta iya biyan abinda Palace din take bukata sai dai kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ma tana zawarcinsa.

Exit mobile version