Umar A Hunkuyi" />

Wulakanta Alkur’ani: Zamfara Za Ta Kafa Dokar Kisa Ga Masu Aikata Hakan

Zaben Cike Gurbi

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya ce gwamnatin sa kwanan nan za ta fitar da wata doka wacce za ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin wulakanta Alkur’ani Mai Girma a cikin Jihar.

Gwamnan ya fadi hakan ne a lokacin da yake karban rahoton kwamitin da gwamnatin Jihar ta kafa domin ya sake nazarin ma’aikatar harkokin Addini, a karkashin shugabancin tsohon mataimakin gwamnan Jihar Mallam Ibrahim Wakkala Muhammad.

Matawalle ya ce, yana cike da bakin ciki a kan yanda wasu mutane suke aikata mummunan aikin wulakanta Alkur’anin a cikin Jihar.

Ya bayyana cewa, a kokarin kawo karshen wannan mummunan aikin, gwamnatin sa kwanan nan za ta zartas da wata doka da ta tanadi yin hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da hannu a kan irin wannan aikin a cikin Jihar.

Ya kara da cewa, za kuma a sanya ido sosai a kan alkalan  kotunan Shari’ar Musulunci domin a ga yanda su ke tafiyar da ayyukan na su, domin akwai hukunci mai tsanani a kan duk alkalin da bay a yin hukuncin yanda ya dace.

Matawalle ya kuma yi roko ga Malaman Musulunci a Jihar da su wayar wa da jama’a kai a kan mahimmancin zaman lafiya, hadin kai da nisantar aikata laifuka.

Matawalle ya kuma tunatar da al’ummar Jihar a kan mahimmancin yin tuba daga aikata laifuka da kuma komawa ga Allah.

Tun da farko, shugaban kwamitin, Malam Ibrahim Wakkala, ya yi kira ne da a canza wa hukumar malamai ta Jihar suna zuwa Hukumar bayar da Fatawa ta Jihar Zamfara, wacce za a rika kiran shugabanta da sunan Mufti.

Ya kuma ce akwai bukatar gwamnati ta sake duba dokokin da ake da su, ta inda za a sanya malaman da su ka cancanta masu cikakken ilimin fikihu da na shari’a su yi aiki a matsayin wakilan kwamitin na Mufti.

Wakkala ya kuma shawarci gwamnatin da ta ci gaba da tsare-tsaren ta na habaka tattalin arzikin Jihar, da kawar da talauci gami da yakar duk wani nau’i na matsalar tsaro domin zaman lafiya da ci gaban Jihar.

Daga cikin wadanda suke halarce a lokacin mika rahoton akwai Sakataren gwamnatin ta Zamfara, Alhaji Bala Bello Maru, shugaban ma’aikatan Jihar, Alhaji Kabiru Balarabe, Mai baiwa gwamnan Jihar shawara, Ambassada Bashir Yuguda da babban Sakatare a gidan gwamnatin Jihar, Alhaji Lawali Ibrahim Kaura, da sauran su.

Exit mobile version