Idris Aliyu Daudawa" />

Wutar Lantarki Ta Kashe ‘Yar Kasuwa A Legas

Iyalan marigayya Mutiat Okanlawon suna neman adalci sakamakon wayar wutar lantarki da ya fado mata a yankin Solebo cikin Age da ke karamar hukumar Ikorodu ta jihar Legas. Iyalan sun bayyana cewa, Okanlawon ta hadu da ajalinta ne lokacin da ta je rakiyan kawarta Funmi a ranar Lahadi 9 ga watan Disambar shekarar 2018, inda ta kwashe kwanaki uku a babban asibitin Gbagada kafin ta mutu a ranar Talata 1 ga watan Junairun shekara ta 2019.

Wani wanda lamarin ya auku a gaban idanunsa mai suna Dabid ya bayyana cewa, wayan wutar lantarki ne ya fado wa Okanlawon inda ya yi sanadiyyar mutuwarta, ya kara da cewa nan take ya sanar wa jami’an wutar lantarki da ke Ikeja da su kashe wuta lokacin da lamarin ya auku. Ya ci gaba da cewa, “Na bayyana wa jami’an wutar lantarki da ke Ikeja da su kashe wuta domin wayar wuta ya fado a kan wata yarinya. Okanlawon tana yi wa kawarta rakiya wanda ta ziyarce ta lokacin da wayar ya fado mata. “Lokacin da wayar ya fado mata, nan take ta fadi a kasa, jikinta ya lalace kamar an saka adda an datsa. Ta samu mummumar raunin kona wanda ba ta iya ganuwa ba. “Abin ya yi tsanani ne lokacin da wayar ta fada mata a cikinta inda ya kone mata hanjinta, lebanta da kuma hannayanta, jikinta ma dai duka ya kone illa iyaka wuyanta da fuskanta su ne basu kone ba. mutane sun ji tsoran zuwa wajen ta, amma ni da wani saurayi mun yi amfani da sanda ina muka cire wayar daga jikinta. Kwatsam sai ga saurayinta inda dama an sanar da shi faruwar lamarin, ya zo cikin gaggawa yana ihun neman taimako, ya firgita sosai inda bai ma san abin da zai yi ba, mun amsa makullin motarsa inda muka sakata cikin sannan muka garzaya da ita babban asibitin Ikorodu.”     

‘Yar uwar Okanlawon mai suna Opeyemi Sofu ta bayyana cewa, marigayyar tana da yaro Farhan, tana cin akwakun dafaffen kwai a kullum sakamakon kunar da ta samu na wutar lantarki. Shofu ta kara da cewa, “Daga baya an maida Okanlawon zuwa babban asibitin Gbagada saboda  babban asibitin Ikorodu basu da kayan aiki na musamman wajen jiyar mai kuna. A asibitin ba ta iya yin nunfashi inda aka saka mata na’urar yin nunfashi. Lokita ya bayar da umurnin ta dunga cin akwakun dafaffen kwai tare da kayan lambu a kullum, saboda tana bukatar kayan gina jiki a cikin jikinta.

Exit mobile version