CRI Hausa" />

Xi: Al’adun Gargajiyar Sin Su Ne Tushen Al’ummomin Kasar

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping ya maida hankali matuka kan aikin yada al’adun gargajiyar kasar Sin, ya ce, kyawawan al’adun gargajiya su ne tushen al’ummomin kasar.

Kafin bikin sabuwar shekarar Sinawa a farkon bana, Xi ya taba kai ziyara wani kauyen ‘yan kabilar Miao dake yankin karkarar lardin Guizhou, a lokacin, ya karfafa wa mutanen kauyen gwiwar ci gaba da raya fasahar dinkin hannu ta Miao. Yanzu, sana’ar dinki ta Miao ta samar da guraben ayyukan yi ga ‘yan mata kimanin dubu dari 5, har an sayar da hajojin fasahar dinki ta Miao zuwa kasashe sama da 60.
Kwanan baya, Xi Jinping ya kai rangadin aiki lardin Qinghai, inda ya ziyarci wani kamfanin samar da dardumar Tibet. Dardumar Tibet na da tarihin fiye da shekaru dubu biyu, Xi Jinping ya taba bayyana cewa, raya sana’ar sarrafa dardumar Tibet ya dace da halin da lardin Qinghai yake ciki, zai ba da gudummawa a fannin kawar da talauci, da raya kauyuka, da kuma karfafa hadin kan kabilu daban daban.
Bugu da kari, Xi Jinping ya taba ba da umurnin raya fannin likitancin gargajiyar Sin, ya jaddada cewa, ya kamata mu ci gaba da yada wadannan al’adu, da sabunta fasahohin da abin ya shafa, domin yayata likitancin gargajiya zuwa kasashen duniya. Haka kuma, likitancin gargajiya ya ba da babbar gudunmawa a fannin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, tun daga shekarar 2020.
Xi Jinping ya ce, ya kamata mu ci gaba da raya al’adunmu, ta yadda za su nuna kyawawansu cikin ko wane zamani.
Cikin ‘yan shekarun nan, sau da dama, Xi Jinping ya sha jaddada muhimmancin musayar al’adu a tsakanin kasar Sin da kasashen duniya, ya kuma gabatar da ra’ayin kasar Sin a fannin yin mu’amalar al’adu, domin maida martani kan ra’ayin “sabanin al’adu”.
A watan Mayun shekarar 2014, Xi Jinping ya kira taron karawa juna sani na kwararrun kasashen ketare a birnin Shanghai na kasar Sin. A yayin taron, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya dace kowace kabila da kowace kasa su koyi kyawawan al’adu na sauran kabilu da sauran kasashe. Al’ummomin Kasar Sin za su ci gaba da koyon kyawawan al’adu da fasahohi na al’ummomin kasashen duniya.
Ya ce, kasar Sin tana son ba da gudunmawa ga bunkasuwar kasashen Asiya, har ma da kasashen duniya baki daya. A nan gaba, za ta kara bude kofarta, domin raya al’adunta kamar yadda ake fata, ta yadda za ta ba da gudummawa ga ci gaban kasashe daban daban. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

Exit mobile version