A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da shugaban majalisar kasashen Turai António Luís Santos da Costa, da shugabar kwamitin kungiyar kasashen Turai ko EU Ursula von der Leyen, sun aikawa juna sakon taya murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da kungiyar EU.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, dangantakar da ke tsakanin Sin da EU ta zama daya daga cikin dangantaka mafi tasiri dake tsakanin bangarori biyu a duniya, kuma ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen kyautata jin dadin jama’ar Sin da kasashen Turai, da sa kaimi ga zaman lafiya da ci gaban duniya. Kamata ya yi kasar Sin da kungiyar EU su tsaya tsayin daka kan ra’ayin bangarori daban-daban, da tabbatar da adalci, da nuna adawa da cin zarafi na bai daya, da hada kai don tunkarar kalubalen duniya.
Shugabannin kungiyar EU sun bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu na rashin tabbas da sauye-sauyen yanayi a duniya, kungiyar EU na son zurfafa dangantakar abokantaka da kasar Sin, da karfafa mu’amala da hadin gwiwa, don inganta zaman lafiya, da tsaro, da wadata da ci gaba mai dorewa a duniya.(Safiyah Ma)