A yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugabannin kasashe biyar na tsakiyar Asiya sun halarci bikin rattaba hannu tare da sanya hannu kan yarjejeniyar Astana ta taron kolin kasar Sin da yankin tsakiyar Asiya karo na biyu, da kuma yarjejeniyar kyakkyawar makwabtaka da abota da kuma hadin gwiwa na dindindin.
Har ila yau, sun kuma halarci bikin kaddamar da cibiyar hadin gwiwa da dandalin tattaunawa na tsakiyar Asiya da kasar Sin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)