Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Masar Da Iran
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Masar Da Iran

byCGTN Hausa and Sulaiman
12 months ago
Xi

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Masar Abdel Fattah al Sisi a daren jiya Laraba a Kazan na Rasha, yayin da yake halartar taron shugabannin BRICS.

Xi ya taya Masar murnar shiga taron a matsayin mamba a karon farko. Ya kuma jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu su kara azama wajen raya dangantakarsu zuwa huldar kafa kyakkyawar makomarsu ta bai daya a zabon zamani. Sin na fatan kara hadin gwiwa da Masar don ingiza bunkasuwar kasashen BRICS mai dorewa da karfafa karfin kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasuwa, da ma kiyaye muradun kasashe masu tasowa.

  • An Gudanar Da Taron Tattaunawar Kafofin Watsa Labarai Na Kazan Na Kasashen BRICS
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawar Kafofin Watsa Labarai Na Kazan Na Kasashen BRICS

A nasa bangaren, Abdel Fattah al Sisi ya nuna godiya ga goyon bayan da Sin ta nunawa kasarsa wajen shiga tsarin BRICS. Yana mai fatan kara tuntubar kasashen biyu a mabambantan bangarori, da ma kiyaye muradun kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasuwa cikin hadin kai, da kuma ingiza kafa tsarin daidaita harkokin duniya bisa adalci da daidaici.

Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun yi musanyar ra’ayi game da halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya. A ganin Xi, batun Palasdinu muhimmin batu ne ga matsalar gabas ta tsakiya. Abin da ake sa gaba shi ne, a yi iyakacin kokarin aiwatar da kudurorin da aka zartas a yayin tarukan kwamitin sulhu na MDD, da gaggauta tsagaita bude wuta a wurin. Tabbatar da tsarin “kafa kasashe biyu” ita ce hanya daya tilo da za a bi wajen warware wannan matsala bisa adalci a duk fannoni mai dorewa.

Kazalika, an ba da labari cewa, a wannan rana da yamma, Xi ya gana da takwaransa na kasar Iran Masoud Pezeshkian. Yayin ganawar tasu, Xi ya nanata cewa, Sin ba za ta sauya matsayinta na sada zumunta da hadin gwiwarta da Iran ba, duk da sauye-sauyen yanayi da ake fuskanta a shiyya-shiyya da ma duk duniya baki daya. A nasa bangaren kuwa, Pezeshkian ya ce, Iran na fatan ita da kasar Sin za su goyi wa juna baya kan wasu muradu masu tushe na kasashen biyu, da ma yaki da babakere tare. Yana godiya ga goyon bayan da Sin take nunawa kasar na shiga tsarin BRICS. Yana mai fatan kara hadin gwiwarta da Sin mai zurfi a dandaloli masu gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban ciki har da BRICS. (Amina Xu)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Ministan Tsaro Ya Jinjina Wa Gwamnan Zamfara, Ya Sha Alwashin Kawo Karshen ‘Yan Bindiga 

Ministan Tsaro Ya Jinjina Wa Gwamnan Zamfara, Ya Sha Alwashin Kawo Karshen 'Yan Bindiga 

LABARAI MASU NASABA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version