Yau Talata, aka gudanar da taron koli a tsakanin kasar Sin da kasashen tsakiya da na gabashin Turai ta kafar bidiyo, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya shugabanci taron tare da gabatar da muhimmin jawabi.
A yayin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai suna nacewa ga mutunta juna, kuma suna hada kai ba tare da gindaya sharudda a fannin siyasa ba, kana Sin tana zaman daidai wa daida a tsakaninta da manya da kananan kasashe, da kuma tattaunawa tare kan manyan manufofin hadin kai, kafa dandalin hadin kai tare da kuma more nasarorin da aka cimma kan hadin kai.
Kasar Sin da kasashen tsakiya da na gabashin Turai suna cike da imanin cewa, yadda suke bude kofa ga juna, zai samar da damammaki kuma yadda suke hakuri da juna, zai taimaka wajen kara cudanya a tsakanin sassa daban daban, kuma wannan shi ne babban tushen kiyaye hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen dake tsakiya da gabashin Turai.
Baya ga haka, Xi Jinping ya nuna cewa, kasar Sin na shirin shigowa da kayayyaki da darajarsu ta zarce dala biliyan 170 daga kasashen na tsakiya da gabashin Turai a cikin shekaru biyar masu zuwa, da nufin habaka shigowa da kayayyaki daga kasashen.
Kana kuma Xi Jinping ya jaddada cewa, kasarsa za ta gaggauta kafa sabon tsarin ci gaba wanda zai mayar da hankali kan raya tattalin ariki a cikin gida don hade kasuwar cikin gida da ta ketare, domin samun ci gaba mai dorewa. Yadda kasar Sin ke samun dauwamammen ci gaba da yadda take bude kofa ga ketare, zai kara karfin farfadowa da kuma ci gaban tattalin arzikin duniya, kana zai habaka hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.
Har illa yau, Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Serbia ta riga ta samu alluran rigakafin COVID-19 miliyan 1 daga kamfanonin kasar Sin, yanzu kuma kasar Hungary tana hadin gwiwa da kamfanonin rigakafin na kasar ta Sin. Dukkan kasashen dake tsakiya da gabashin Turai da suke bukatar hadin gwiwa a fannin allurar rigakafi, a shirye kasar Sin take ta himmatu wajen yin la’akari da haka.
A watan Afrilu na shekarar 2012, aka fara shirya tattaunawa a tsakanin shugabannin kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai a Poland, kuma tun daga wannan lokacin, aka bullo da tsarin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a hukumance. Haka kuma tun bayan da aka kafa wannan tsari, cinikayya a tsakanin bangarorin biyu ya karu zuwa kashi 8 cikin 100, adadin da ya ninka sau 3 da wani abu, ya zuwa shekarar 2020 inda darajarsa ta zarce dala biliyan 100. (Mai fassara: Bilkisu)