Connect with us

RAHOTANNI

Xi Jinping Ya Taya CCTV Murnar Cikon Shekaru 60

Published

on

A lokacin cika shekaru 60 na kafuwar Gidan Talibijin na kasar Sin na CCTV, watau kafuwar sana’ar talabijin bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping ya aike da sakon taya murna a madadin kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin.

Xi Jinping ya ce, aikin talabijin muhimmin bangare ne cikin harkokin watsa labarai na JKS. Kana, cikin shekaru 60 da suka gabata, bisa jagorancin JKS, masu aikin talabijin sun ba da gudummawa matuka wajen raya harkokin al’umma da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin.

Haka kuma, ya ce, bayan kafuwar Babban Gidan Rediyo da Talibijin na kasar Sin na CMG, an dukufa wajen tsara shirye-shirye masu kyau bisa jagoranci na kwamitin tsakiya, domin sabunta ayyukan yada labarai ga ketare, da kuma nuna ainihin kasar Sin yadda ya kamata ga sassan duniya.

Xi ya nuna fatan cewa, ya kamata ma’aikatan CMG, da masu aikin talibijin na kasar Sin su kara saninsu game da ka’idojin tsarin gurguzun musamman na kasar Sin a sabon zamani, da kuma ra’ayoyin cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 19, domin karfafa ayyukan yada labarai ga kasa da kasa, da yin kwaskwarima yadda ya kamata, ta yadda za a kafa wata babbar kafar yada labarai mai ba da karfin tasiri ga kasa da kasa.

A safiyar yau Laraba, CMG ya kira bikin murnar cika shekaru 60 da kafuwar sana’ar talibijin a nan birnin Beijing, inda aka gabatar da sakon taya murna da shugaba Xi Jinping ya aiko. (Mai Fassarawa: Maryam Yang, ma’aikaciyar sashen Hausa na CRI)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: