Daga CRI Hausa
Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kolin JKS Xi Jinping, ya bayyana a jiya Talata cewa, lafiyar al’umma muhimmiyar alama ce ta yanayin jin dadin rayuwar su.
Xi wanda ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci wani asibiti da ke birnin Sanming, dake lardin Fujian na gabashin kasar Sin, ya ce kasar sa ta ci gaba da samun bunkasuwar fannin kiwon lafiya, tun daga shekarar 1949, lokacin kafuwar jamhuriyar kasar Sin, kuma nasarar da kasar ta cimma a wannan fanni ta dara ta wasu daga kasashe masu ci gaba, musamman a fannin karuwar matsakaicin tsawon rayuwar al’umma. Ko da yake ya yi nuni da cewa, kawo yanzu, ba a kai ga cimma daidaito a ci gaban fannin ba da hidimar kiwon lafiya tsakanin sassa daban daban na kasar ba.
Shugaban na Sin ya kara da cewa, yayin aiwatar da shirin shekaru biyar biyar na tsarin samar da ci gaban kasar na 14, wato tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, Sin za ta kara azama wajen mayar da jama’a da lafiyarsu gaban komai, za kuma a ci gaba da zurfafa gyare gyare a fannin kiwon lafiya, ta yadda ba bukatar Sinawa su yi tafiya mai nisa domin samun jinya.
A jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci gundumar Shaxian dake karkashin birnin Sanming, yayin rangadin da yake yi a lardin Fujian na gabashin kasar Sin, inda ban da asibitin, ya kuma yada zango a kauyen Yubang, da kuma cibiyar hada hadar hakkin mallakar hajojin gundumar Shaxian, inda ya ganewa idanun sa irin matakan da ake aiwatarwa, game da raya karkara da gyaran tsarin ikon mallakar gandayen daji. (Saminu)