CRI Hausa" />

Xi: Sin Za Ta Ci Gaba Da Raya KasaTa Hanyoyin Kare Muhalli

“Nasarorin da kauyen Yu ya cimma sun nuna cewa, hanyar da yake bi wajen neman bunkasuwa ta hanyoyin kiyaye muhalli ta yi daidai”. Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da jama’ar kauyen, a lokacin da yake rangadi a kauyen Yu na gundumar Ji’an dake lardin Zhejiang na kasar Sin.

Xi Jinping ya kai ziyara a lardin Zhejiang ne a wannan lokaci na musamman, inda a halin yanzu, kasar Sin ke dukufa wajen hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, a sa’i daya kuma, al’ummar kasa suna gaggauta komawa bakin ayyukan su, domin cimma burin da kasar ta sanya a bana, na raya tattalin arziki, da zaman takewar al’umma, ta yadda za a kafa wata zamantakewar al’umma mai wadata bisa dukkan fannoni. Ba kawai ana neman raya tattalin arziki ba, har ma an mai da kare muhalli wani muhimmin aiki yayin da ake kokarin raya zamantakewar al’ummar Sin.
Game da batun raya tattalin arzikin kasar Sin kuwa, neman bukasuwa ta hanyar kare muhalli ya samar da sabbin bukatu ga al’ummar kasa, da ma sabbin damammaki wajen neman ci gaban tattalin arziki. Kuma bisa sakamakon kididdigar da hukumomin da abin ya shafa suka fidda, an ce, ya zuwa shekarar 2025, darajar kayayyaki, da masana’antu masu kiyaye muhalli za su samar, zai kai RMB biliyan dubu 12 a kasar Sin, adadin da zai kai kaso 8% cikin ma’aunin tattalin arziki na GDP na kasar. Ya zuwa shekarar 2035 kuma, adadin zai kai sama da 10% na GDPn. Kana, wasu masana ilimin tattalin arziki sun yi hasashen cewa, a nan gaba kuma, kasar Sin za ta zama dogaro kan harkokin kiyaye muhalli wajen raya tattalin arzikinta.
“Za mu ci gaba da kyautata muhalli, da samun matukar karuwar tattalin arziki.” Wannan shi ne alkawarin da kasar Sin ta yi, wanda ya nuna aniyar kasar Sin, wajen neman ci gaba, tare da samar da Karin gudummawa ga kasashen duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

Exit mobile version