Xi: Sinawa Na Burin Ganin Al’ummun Duniya Na Rayuwar Farin Ciki Da Lumana

Daga CRI Hausa,

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Asabar cewa, kasar Sin ba kawai tana bukatar samun zaman lafiya da hadin kan al’ummarta ba ne har ma tana burin ganin zaman lafiya da lumana ya wanzu a dukkan kasashen duniya domin samun cigaba na bai daya.

Xi, yayi wannan tsokaci ne yayin gabatar da jawabi a taron murnar cika shekaru 110 da gabatar da juyin jiya halin shekarar 1911.

Shugaba Xi yace, “Tayar da tarzoma da mulkin danniya baya daga cikin dabi’un Sinawa. Burin al’ummarmu shi ne cimma nasarar bunkasa cigaban kasa, ban da wannan ma Sinawa suna burin ganin dukkan al’ummun duniya sun yi zaman rayuwa ta farin ciki da lumana.”
Shugaban na Sin ya ce, zangon tafiyar da aka sanya gaba shi ne, kasar Sin a ko da yaushe za ta cigaba da kafa tutar wanzar da zaman lafiya, da bunkasuwa, da hadin gwiwa, da cin moriyar juna, da tsayawa tsayin daka wajen gina tsarin cigaban al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama, da kuma kokarin inganta salon shugabancin duniya.(Ahmad)

 

Exit mobile version