Yayin da ake gab da yin bikin ranar malamai ta kasar Sin karo na 41 nan ba da jimawa ba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da martanin wasika ga wakilan malamai na musamman a duk fadin kasar, inda ya bayyana fatansa tare da mika gaisuwar ranar ga malamai da ma’aikata a bangaren ilmi a fadin kasar.
A cikin wasikar, Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru 20 da fara aiwatar da shirin “malamai na musamman”, da yawa daga cikin malamai na musamman sun dukufa wajen ba da ilmi a yankunan karkara, tare da nuna kishi da jajircewa. Ya kuma bayyana fatan cewa za su ci gaba da tabbatar da aniyarsu kan koyarwa tare da bayar da sabbin gudumawa wajen inganta farfado da yankunan karkara da gina kasa mai karfi a fannin ilimi.
Shirin “malamai na musamman”, wanda aka gudanar da shi a makarantun wajibi na karkara, shiri ne da aka kafa da kudade na musamman daga gwamnatin kasar don daukar wadanda suka kammala karatu a jami’a a matsayin malamai masu koyarwa a makarantun karkara na yankunan tsakiya da yammacin kasar Sin. (Safiyah Ma)