A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci hada karfi da karfe wajen gina yankin Xinjiang ya zama mafi kyau a cikin tsarin zamanantar da kasar Sin. Ya bukaci hakan ne yayin da ya gana da wakilai daga dukkan kabilu da sauran fannonin rayuwar al’umma a yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na arewa maso yammacin kasar Sin.
Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya isa birnin Urumqi, babban birnin yankin Xinjiang da safiyar yau, domin halartar bukukuwan cika shekaru 70 da kafuwar yankin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)