Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga kungiyoyin matasa da na dalibai da su kiyaye bin tsarin siyasa mai kyau, da zurfafa yin gyare-gyare da kirkire-kirkire, kuma su samar da sabbin nasarori a sabuwar tafiya a karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin.
Xi, wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya bayyana hakan ne a cikin wata wasikar taya murna ga taron babbar kungiyar matasan kasar Sin da kuma taron babbar kungiyar daliban kasar Sin, wanda aka bude a safiyar yau Laraba a birnin Beijing. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)