Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kasarsa a shirye take ta yi aiki tare da Sifaniya, wajen gina dangantaka mai karin juriya bisa matsayin koli, kuma mai game sassa daban daban a dukkanin fannoni, wadda za ta yi matukar tasiri a tsakanin kasa da kasa.
Shugaba Xi, ya bayyana hakan ne a Larabar nan a birnin Beijing, yayin da yake tattaunawa da sarkin Sifaniya Felipe VI, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin.
Wannan ne dai karon farko da sarki Felipe VI ke ziyara a kasar Sin tun bayan darewa karagar mulki, kana karon farko da wani basaraken Sifaniya ya ziyarci kasar Sin cikin shekaru 18.
Kafin ganawar ta su, shugaba Xi ya shiryawa sarki Felipe VI bikin maraba da zuwa. Kana bayan tattaunawar, shugaba Xi da sarki Felipe VI, sun halarci bikin sanya hannu kan takardun hadin gwiwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














