Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada kokarin sa kaimi ga ciyar da shirin kasar Sin mai kwanciyar zuwa matsayi mai girma.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS a jiya Juma’a. Inda ya yi kira da a ci gaba da kokarin kyautata zaman lafiya a kasar, al’umma su kasance cikin tsari, da kara inganta gudanar da mulkin kasar, kuma jama’a su samu karin gamsuwa. (Mohammed Yahaya)