CRI Hausa" />

Xi Ya Saurari Rahoton Aikin Gwamnatin Yankunan Hong Kong Da Macao

A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya saurari rahoton aikin gwamnati na yankin musamman na Hong Kong na shekarar 2020, da jagorar yankin Carrie Lam ta gabatar da kafar bidiyo. Haka kuma a yau din ne shugaba Xi ya saurari rahoton aikin gwamnati na yankin musamman na Macao na shekarar 2020 da jagoran yankin Ho lat Seng ya gabatar da ma yanayin da yankin yake ciki a halin yanzu.

A jawabinsa, Xi ya yabawa jagorar yankin Hong Kong Carrie Lam, kan matakin da ta dauka, musamman game da dokar tsaron kasa, da yadda ta sauke nauyin dake bisa wuyanta, da irin kauna da ta nunawa kasarta da kuma yankin na Hong Kong. Yana mai cewa, gwamnatin tsakiya, ta yi na’am da rawar da ta taka wajen gudanar da ayyukanta kan harkokin da suka shafi yankin na Hong Kong.
Bugu da kari, shugaba Xi ya yaba wa kwazon jaroran yankin Macao, da matakan da ya dauka wajen kandagarkin yaduwar annobar COVID-19, da managartan matakan farfado da tattalin arziki da ragewa jama’a wahalhalu, matakan da shugaba Xi ya ce, sun haifar da sakamako masu kyau da inganta rayuwar jama’a a yankin. Kana gwamnatin tsakiya ta yaba da irin aikin da ya yi a yankin.(Mai fassatawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

Exit mobile version