Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tare da kasashe makwabta, da kuma kokarin bude sabon babi na ayyukan da suka shafi kasashe makwabtan kasar Sin.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin kolin soja na kasar, ya bayyana hakan ne a taron koli kan ayyukan da suka shafi kasashe makwabta, wanda aka gudanar a birnin Beijing daga ranar Talata zuwa Laraba. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)