Xi Ya Yi Rangadi A Nanyang Dake Lardin Henan

Daga CRI Hausa

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar, a ranar Laraba ya kai ziyarar aiki birnin Nanyang dake tsakiyar lardin Henan na kasar Sin.

Da yammacin wannan rana, Xi ya fara da ziyartar ginin da aka kebe don tunawa da Zhang Zhongjing, tsohon shahararren masanin kimiyyar hada magungunan gargajiyar kasar Sin, kana masanin kimiyya na gabashin daular Han tsakanin tsakara ta 25 da ta 220. Xi ya karanta tarihin rayuwar Zhang da irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban magungunan gargajiyar kasar Sin.
Daga bisani Xi ya zarce zuwa lambun shan iska na Rosa Chinensis, ko kuma Chinese rose, sannan ya ziyarci wani kamfanin yankin na mugwort wanda ke sarrafa magungunan gargajiya. Bugu da kari shugaba Xi ya kuma duba yadda mazauna birnin Nanyang ke amfani da furanni wajen hada magungunan gargajiya domin bunkasa kamfanonin wurin, da bunkasa samar da guraben ayyukan yi ga mazauna wurin. (Ahmad)

Exit mobile version