Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NAZARI

Yaƙi Da Boko Haram: Ko Ziyarar Buhari Jihar Borno Na Da Tasiri?

by Tayo Adelaja
October 7, 2017
in NAZARI
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammed Maitela

A safiyar ranar lahadin da ta gabata ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kai wata ziyarar ba-zata, a jihar Borno tare da gudanar da bikin cikar Nijeriya shekara 57 da samun yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Ziyarar wadda ake kallon ta a matsayin wadda aka keɓanci jami’an tsaron Nijeriya masu fito-na-fito da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da ita, tare da ƙara musu azama da karsashi, da tasiri ga jama’ar yankin, kuma girmama wa ce zaratan sojojin Nijriya waɗanda suka ɗauki lokaci suna yaƙi da yan ta’adda a fagen fama.

Bugu da ƙari kuma, ziyarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a daidai irin wannan lokacin zai sake buɗe sabon shafi ga alƙiblar ƙasar wajen ganin ta cimma muradun da ta sa gaba na yaƙi da take da yan tarzomar Boko Haram a jihar dama yankin baki ɗaya. Musamman halin kwan-gaba kwan-baya da ake samu a fagen cin galabar mayaƙan; yayin da a lokuta da dama gwamnatin ta sha yin iƙirarin cewa ta gama da mayaƙan amma sai daga baya su sake ɓulla ko kai munanan hare-haren da ke jawo asarar rayukan jama’a.

A hannu guda kuma zata taimaka wajen sauran ƙorafe-ƙorafen jama’an tsaron wanda a baya sun sha bayyana cewa gwamnati tana jan ƙafa tare da yin sako-sako da lamarin. Baya ga yadda wannan matsalar ke jawo asarar rayukan yan Nijeriya haɗi da jami’an tsaron, haka kuma al’amarin ya jawo sama mutane miliyan biyu ƙaurace wa muhallin su, yayin da adadi mai yawa ke zaune a sansanonin yan gudun hijira. Kana kuma da yadda abin ke neman ya gagari kundila. Duk da ba haka yan Nijeriya suke tsammani a wannan gwamnati ta shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba, musamman yadda tsanantar matsalar tsaro ta jawo wa jam’iyyar PDP baƙin jini a lokacin zaɓen 2015.

Manazarta sun sha bayyana ra’ayoyin su dangane da yadda ake yiwa sha’anin tsaron riƙon sakainar kashi, kana da rashin ɗaukar sahihan hanyoyi wajen tunkarar matsalar daga ɓangaren gwamnatin tarayya. Duk da yadda yake nauyin tafiyar da sha’anin tsaron ƙasa yana bisa wuyan jami’an tsaro, to amma kuma bin bahasin bayanan sa kuma yana bisa dokin wuyan fadar shugaban ƙasa.

Yan Nijeriya sun zaci cewa baya ga umurnin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya baiwa manyan hafsoshin sojan Nijeriya; kan cewa su tattara nasu-ya-nasu su koma Maiduguri da zama domin tunkarar matsalar tsaro, an zaci cewa shugaban ƙasa zai rinƙa kai irin wannan ziyarar ba-zata, lokaci bayan lokaci. Duk da yake wasu na ganin rashin tafiyar da ya sha fama da ita ne ta kawo cikas.

Masana suna kallon wannan matsala ta tsaro ba al’amari ne wanda ake saku-saku dashi bane; ballantana fadar shugaban ƙasa ta harɗe ƙafafu tana dakon bayanai akan sa kawai. Saboda ko ba komai, ta hanyar irin waɗannan ziyarori ne kaɗai zai sa a jefi tsuntsu biyu da dutsi ɗaya; bayan shaidar abinda ke wakana, kuma zata ƙarfafi gwiwar jami’an tsaro waɗanda suka sadaukar da rayukan su wajen kare ƙasa da yan ƙasa.

Hasashen da jama’a da dama ke yi a kan muhimmancin wannan ziyara wadda ya kai a yankin arewa maso-gabas shi ne akwai yuwuwar ta canja alƙibla da fasalin wannan yaƙi da Nijeriya take yi da yan ƙungiyar Boko Haram, ta duba da cewa a matsayin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na tsohon soja zai fahimci abubuwa da dama a kan.wannan matsalar sannan ya jinjina ta da rahotanin da ke samun sa a ofis, alabaahi ya ɗauki mataki.

A cikin wannan muhimmiyar ziyara shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya samu gagarumar tarba a filin jirgin Maiduguri; yayin da gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima da babban hafsan ma’aikatar tsaro ta ƙasa Janar AG Olonisakin da sauran hafsoshin rundunar. Had wala yau da shugaban hukumar yan-sandan cikin, Lawal Usman Daura da manyan jami’an gwamnati.

Saukar shugaban ke da wuya ya wuce zuwa barikin Maimalari inda ya kalli faretin girmamawa daga kwamandan rundunar sojan Nijeriya mai yaƙi da yan ta’addan Boko Haram ta ZAMAN LAFIYA DOLE.

Bayan da ya kammala duba faretin girmamawar keda wuya sai ya zarce zuwa Barikin Bataliya ta 212 inda aka shirya nan ne za a gudanar da bikin tunawa da ranar samun yancin kan Nijeriya daga Turawan mulkin mallaka. Wanda kafin wannan lokacin ya ɗauki harramar yan soja. Yayin da isar babban kwamandan askarawan Nijeriya ; Muhammadu Buhari, keda wuya ne muhallin ya ɓarke da sarewa da bogala tare da tilawar taken Nijeriya daga bakin Mista Abiodun Koya (ɗan Amurika).

Har wala yau kuma, a cikin jawabin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taɓo batutuwa da dama da suka ƙunshi kalaman jinjina ga ƙoƙarin jami’an tsaron dangane da biyayya sau-da-ƙafa ga dokoki da tsari kana da sadaukarwar da suka bayar wajen kare ƙasa. Bugu da ƙari kuma ya ɗauki akƙawarin marawa jami’an tsaron Nijeriya da duk abinda zai ƙara musu karsashi wajen sauke nauyin kare ƙasa da al’ummar ta, cikin ayyukan su.

A daidai wannan gaɓa ne shugaban ƙasa tare da gwamnan jihar Borno, shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin tarayya da hafsan ma’aikatar tsaro dana yan-sandan ciki, Shehun Borno da manyan jami’an gwamnati ne suka jagoranci yanka ƙaragon bikin cikar Nijeriya shekaru 57 da yancin kai.

Haka zalika kuma, shugaban ya ziyarci baje-kolin nuna makamai wanda ɓangaren sojan sama suka ƙayata bikin dashi. Makaman sumfurin F-7Ni, Alpha Jets, L-39ZA, Mi-35, Mi-17, da Agusta 109 LUH. Yayin da kuma shugaban ya duba nau’in makaman yaƙi irin su Armoured Fighting Ɓehicles (AFƁs) da sumfurin bindigogin Artillery. Kafin ya koma Abuja; a cikin wannan ziyara ta yini ɗaya.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Zamu Ɗauki Mummunan Mataki Kan Kamfanin Mulmula Ƙarafa Na Katsina —Kungiyar Kwadago

Next Post

Gwamnonin Farar Hula A Kano: Wa Ya Biya Bashi, Wa Ake Bi?

RelatedPosts

Android

Muhimman Hanyoyi Don Kare wayar ‘Android’ Daga Kutse (II)

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Ibrahim Sabo (ibnsabo15@gmail.com), Manyan masana sun shaida cewa duk...

Tsaron Arewa

Har Yanzu A Kan Matsalar Tsaro A Arewa

by Muhammad
2 days ago
0

Kwamared Sunusi Mailafiya, alimailafiyasunusi@gmail.com - 08036064695; Shugaba Buhari ya umarci...

Mata

Yadda Mata Suke Jefa Yan’uwansu Mata Cikin Halaka ta Hanyar Tura Su Gidajen Aiki

by Muhammad
3 days ago
0

A yayin da hukumomi suke ƙokarin suga sun magance safarar...

Next Post

Gwamnonin Farar Hula A Kano: Wa Ya Biya Bashi, Wa Ake Bi?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version