Yaƙi Da Cin Hanci Da Rashawa A Nijeriya, Anya Kuwa?

Yasir Ramadan Gwaleyasirramadangwale@gmail.com          +23408099272908

Batun cin hanci da karɓar rashawa, kusan muna iya cewar shi ne ummul haba’isin rushewar gwamnatin Goodluck Jonathan a zaɓen 2015. Idan ban da batun Boko Haram da yayi tsanani lokacin Gwamnatin Jonathan, to batun da ke kan gaba wanda ake zargin ya yi wa gwamnatin Jonathan ɗin ɗaurin butar Malam shi ne batun cin hanci da rashawa.

Kusan bayanai sun nuna cewar shugaba Jonathan ya dabaibaye kansa da mutanan da suka shaƙa har wuya ta fannin cin hanci da rashawa. Wannan ta sanya ake masa ganin babu wani kataɓus da zai iya yi a harkar yaƙi da cin hanci da rashawa, shi yasa da dama tun bayan barin Malam Nuhu Ribadu daga hukumar EFCC suka cire tsammanin za a yi wani abin kirki ta fannin yaƙi da cin hanci da rashawa.

Cin hancin da ake yi a zamanin Gwamnatin Shugaba Jonathan bai ƙara bayyana ba, sai lokacin da tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Sarkin kano Muhammadu Sunusi na biyu, ya riƙa fitowa fili ɓalo-ɓalo yana kwarmato akan yadda miliyoyin kuɗaɗen daloli suka riƙa yin layar zana a Gwamnatin.

Musamman a ma’aikatar man fetur wadda ke zaman zuciyar gwamnatin Nijeriya.

Sanusi Lamido Sanusi na lokacin wanda yanzu Muhammadu Sunusi na biyu, ya kwarmata bayanan batan wasu kuɗaɗe da suka kai kimanin dalar Amurka biliyan 20 wanda waɗannan kuɗaɗe malalane gashin tinkiya. Wannan na daya daga cikin abin day a ja hankalin ‘yan Nijeriya cikin gida da waje, na irin kazamin cin hancin da ake yi a zamanin gwamnatin Jonathan, kuma wannan batu na zargin cin hanci da aka riƙa yi a ma’aikatar Mai ta ƙasa ya taimaka wajen kifewar Gwamnatin Jonathan.

Sabida korafe korafe akan cin hanci da rashawa a ma’aikatar Mai ta Nijeriya, har sai da ta kai Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya kafa wani kwamati karkashin jagorancin tsohon shugaban hukumar yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta EFCC , Nuhu Ribadu, domin ya duba irin kuɗaɗen da ake samu a ma’aikatar Mai ta tarayya da kuma yadda ake sarrafa waɗannan kuɗaɗe. Kwamatin Nuhu Ribadu yayi aikinsa kuma ya fito da bayanai masu cike da ban mamaki kan irin yadda ake sata da zarmiya da rubda ciki da dukiyar Nijeriya a ma’aikatar Man fetur ta Nijeriya.

A wannan lokacin da cin hanci ya kai makura a Nijeriya, mutane da yawa ciki da wajen Nijeriya, sun yabawa shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a lokacin sabida yadda yayi namijin kokari wajen zabo Malam Nuhu Ribadu ya nada shi shugaban wannan kwamiti, duba da yadda Ribadu din yake da tarihin yakar cin hanci da rashawa, musamman lokacin da yake shugaban hukumar EFCC, wannan ta sanya wasu ke ganin an kuduri aniyar fara shawo kan matsalar cin hanci da rashawa a Nijeriya.

Sai dai ba’a je ko ina ba, aka koma gidan jiya, bayan da Nuhu Ribadu ya kammala aikinsa kuma ya mika rahoto, babu wani abu day a canza a ma’aikatar man fetur ta ƙasa, musamman na irin kwangilolin da ake bayarwa, da kuma kamfanonin da ake baiwa kwangilar. Wannan batu na daya daga cikin abin da ya damu ‘yan Nijeriya a rai cikinta da wajenta, yadda wasu mutane su kadai ke azurta kansu da dukiyar ƙasa.

Wannan c eta sanya da aka buga gangar siyasar 2015, mutane suka gwammace Muhammadu Buhari da yayi ta nanata batun yaƙi da cin hanci da rashawa a lokacin da yake yawon neman a zaɓe shi a matsayib shugaban ƙasa. ‘Yan Nijeriya da dama, ciki da waje, sunyi amanna da canjin da Muhammadu Buhari yayi alƙawarin kawowa, da kuma aniyarsa ta yaƙi da cin hanci da rashawa a gwamnatance.

Ba tare da wata wata ba, Buhari ya samu soyuwa a zukatan ‘yan Nijeriya, suna fatan zai fidda suhe daga wuta, idan ya zama shugaban ƙasa ya kawo karshen cin hanci da rashawa da yayi katutu a kowanne fanni na Gwamnati.

Wannan ceta sanya amon canji ya game tare da karaɗe ƙasarnan ko ta ina, inda mutane ke fatan ganin ansamu canji wanda zai kawo karshen cin hanci da rashawa, musamman kuma ga mutumin da ake kyautata masa zaton cewar zai iya aikin, ganin cewar yana daga cikin mutane da ba’a musu zargin tara dukiyar haram. Batun yaƙi da cin hanci da rashawa, shi ne fitila kuma shi ne linzamin yaƙin neman zaɓen Muhammadu Buhari a jam’iyyarsa ta APC.

A yayin yaƙin neman zaɓe, Jigo kuma kashin bayan wannan zaɓen day a kawo wannan Gwamnati, shi ne batun yaƙi da cin hanci da rashawa da ya dabaibaye ma’aikata da manya manyan jami’an Gwamnati, kusan shi ne babban musabbabin zuwan wannan gwamnati ta canji. Da yawan ‘yan Nijeriya sun zabi wannan Gwamnati ne, bias alƙawarin da akai na cewar za a yi yaƙi da cin hanci da rashawa babu sani babu sabo, kasancewar da dama sun san waye Muhammadu Buhari shi yasa mafiya yawa basu ji wani ko dar ba, akan ikirarin da Jagoran gwamnatin yayi a lokacin yaƙin neman zaɓe na yakar cin hanci da rashawa.

Sai dai ya zuwa yanzu da wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari ta samu wattani 29 da kafuwa, kusan zamu ce anci fiye da rabin wa’adin wannan gwamnati, amma a zahiri babu wani canji da mutane suka gani a harkar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya. Ma iya cewar batun yaƙi da cin hancida rashawa ya zama akwai ‘yan mowa da ‘yan bora, sai ya kasance, duk wanda yake tare da wannan gwamnati duk irin dukiyar haram din day a mallaka, babu rowan hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa das hi, kawai in kaga ana batun yaƙi da masu cin hanci da rashawa to batu ake na wasu ‘yan adawa na wannan gwamnati.

Gwamnati na canji karkashin jagorancin Muhammadu Buhari kamar ta bayanta, ta dabaibaye kanta da wasu mutane da ake ganin suma masu cin hanci da rashawa ne, kuma an barsu suna yin facaka yadda suka ga dama ba tare da tsoro ko shakkar za a iya kama su ba. Barayi da maciya amanar ƙasa, gasu nan ana iya gane su face face a cikin wannan Gwamnatin amma babu wani abu da aka yi musu ko da kuwa na barazana ne, shi yasa sai cin karensu suke yi babu babbaka.

Ana samun ƙazamar cuwa cuwar ɗaukarma’aikata a wannan Gwamnatin, musamman aka ruwaito babban Bankin Nijeriya ya ɗauki ma’aikata ba atre da bin ka’idar ɗaukar ma’aikata ba, inda aka riƙa ganin sunayan ‘ya ‘yan manyan masu rike da ma’aikatun Gwamnati a yanzu a cikin mutanan da aka ɗauka aiki a babban bankin ƙasa. Abin nan da bahaushe kan ce dakan daka shiƙar daka…

Haka nan ita ma hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta ƙasa FIRS daNNPC da sauransu, suma duk sun ɗauki ma’aikata ta barauniyar hanya, ba tare da bin ka’idar ɗaukar ma’aikata ba, kuma galibi ‘ya ‘yan manyan mutane aka ɗauka aiki a waɗannan manya manyan ma’aiktun da ake ganin kusan sune kan gaba wajen samun kuɗi a gwamnati. Wannan duk ya faru ne a Gwamnati da ‘yan Nijeriya suka yi ammana da ita dari bida dari cewar zata yi yaƙi da irin wannan ƙazamar cuwa cuwar, amma abin mamaki sai gashi irin hakan tana faruwa, jagoran gwamnatin da ake kyautata masa zato sama da kowa ya kasa tsawatarwa ko ɗaukar mataki kan irin wannan almundahana da jami’an gwamnatinsa suke tafkawa.

Bayan haka, duk da irin lalacewa da ake gani irin ta Gwamnatin Jonathan sai da ta kori wani ma’aikaci Loius Edozien daga mukamin darakta a ENgeering and Technical Serɓice a ma’aikatar Neja Dalta, sabida almundahana da aka same shi yana tafkawa, amma kuma aka wayi gari wannan Gwamnatinta Muhammadu Buhari ta wanke shi harma ta dawo das hi aiki, mutumin da dukkan bayanai suka tabbatar da cewar mara gaskiya ne, maciyin amanar ƙasa, amma sabida ance yana da kusanci da masu ruwa da tsaki na cikin gida a wannan gwamnatin shi yasa aka dawo das hi ba tare da wata tuhuma ba.

Haka nan kuma, abu na kwanannan shi ne yadda aka samu labarin dawo da Abdulrasheed Maina bakin aikinsa, harma aka yi masa Karin girma. Mutumin da Gwamnatin Jonathan duk da lalacewar tat a kora sabida cin hanci da rashawa, da babakere da dukiyar al’umma a hukumar fanshon ma’aikatan gwamnatin tarayya ta biliyoyin nairori, aka aka wayi gari rana a tsaka, ance an dawo das hi bakin aikinsa.

Bayanai dai sun nuna cewar, Ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau da kuma Antoni Janar kuma Ministan Sharia’ah Abubakar Malami na da hannu dumu dumu wajen dawo da Maina bakin aikinsa, kafin daga bisani a zargi shugabar ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Winifred Oyo-Ita da hannu wajen dawo da Mainaa, zargin da ta musanta, kuma ta dora alhakin abin ga ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau.

Bayan haka, ga batun Sakataren Gwamnatin tarayya Babachir Daɓid Lawal da kuma shugaban NIA da ake zarginsu da arzuta kansu da dukiyar haraam, anyi kwamiti an bincika kuma an gabatarwa da Shugaban ƙasa rahoton binciken, yau kimanin watanni biyu kenan, amma babu wani mataki da aka ɗauka akansu.

Ire iren waɗannan badakaloli da suke cikin wannan gwamnatin da yawa su ne suke sanya, guiwowyin mutane suke sarewa game da gaskiyar batun yaƙi da cin hanci da rashawa a wannan Gwamnatin karkashin Jagorancin Muhammadu Buhari, mutumin da ko kusa ba’a taba yi masa tsammanin za a yi haka a karkashin yayi shiru ba. Sai gashi ana zaton wuta a makera ta tashi a masaka.

Lokaci yayi  ya kusan kurewa wannan Gwamnati wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, domin yanzu haka muna ƙara fuskantar zaɓen 2019 ne, kusan duk abin da ya faru ko zai faru nan gaba, to ana iya masa kallon yana da alaka da zaɓen 209 ne, ko dai domin a yaudari al’umma a nuna cewar da gaske ake, ko kuma, a yaudari mutane domin samun goyon bayansu.

Abin fatan shi ne, kafin ƙarewar wa’adin wannan gwamnati, Shugaba Muhammadu Buhari yayi wani abu wanda al’ummar Nijeriya za su ɗauka da gaske yake yi a lokacin da yake ta ƙalubalantar gwamnatocin da suka gabata kan batun cin hanci da rashawa. Da dama kuma daga cikin waɗan da suka kafa wannan gwamnatin na fargabar kada reshe ya juye da mujiya kan bataun yaƙi da cin hanci da rashawa, abin da Buhari ya yi zargi akansa a baya, shi kuma yanzu ya samu kansa tsamo tsamo a ciki. Fatanmu Allah ya fidda A’I daga rogo.

Exit mobile version