Yaƙi Da Cin Hanci: Dalilan Da Suka Sa EFCC Da ICPC Suke Samun Naƙasu –Akin Olumiji

Daga Abubakar Abba

Tsohon ministan Shari’a kuma Atoni Janar na ƙasa Akin Olujimi ya bayyana cewar yaki da cin hanci da rashawa zai ci gaba da samun naƙasu a ƙasar nan idan hukumomim yaki da cin hanci da rashawa da jami’an tsaro burin su din yin riga Malam Masallace ne kawai zuwa kotu, don bada shaida don a kulle waɗanda ake zargi.

Olujimi ya yi nuni da cewa EFFC da jami’ain tsaro zasu ci gaba da samun naƙasu akan kararrakin da suka shigarwa a gaban kotuna saboda rashin gudanar da cikakken bincike da samar da gamsassun hujjoji akan waɗanda suke zargi don ayi masu hukunci.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi, a taron ƙungiyar ƙwararrun masu Shari’a  ta ƙasa na shekarar 2017 da aka gudanr a jihar Oyo.

Ya shawarci yan Nijeriya da kaɗa su sanya rai akan kotu tayi saurin yanke hukunci akan shari’u dake gaban ta na zargin cin hanci da rashawa.

Olujimi yace, daga shekarar 2003 zuwa yau, duk da cewar EFCC ta yi kamu sun kuma kai waɗanda suka kama gaban kotu, duk da haka ba a daina cin hanci da rashawa sai ƙara zamowa take  ruwan dare.

Olujimi ya ce, “a matsayina na ƙwararre a fannin Shari’a, mun san cewar binciken ƙara bai isa ba, domin Alƙalin baya wurin lokacin da aka yi zargin na cin hancin da rashawa, domin yana dogara ne akan shedu da aka gabatar a gaban kotu.”

Ya ƙara da cewa, shaidar da aka gabatarwa da kotun baza su gamsar da kotun ba, inda hakan ke sanya ALƙalin ya sallami wanda ake zargin.

Ya ci gaba da cewa, yana da mahimmanci EFCC da ICPC su tabbatar sun zurfafa dogon bincike kafin su garzaya zuwa kotu don gamsar da mutanne gari.

Ya yi nuni da cewar su alummar gari abin da suke tunani shi ne Alƙali ya kulle wanda aka gurfanar a gabanta ake zargi a cikin sati ɗaya ko biyu, inda yace hakan ba zai yuwau ba, kuma ba inda aka taɓa yin haka a duniya.

Olujimi ya ce, ƙasar Amurka da Birtaniya zasu iya biyo wanda suke zargi har tsawon shekara kafin su kama shi, sai sun tabbatar sun tattara dukkan hujojin su, kamar samar da lauyoyin su da zasu sanya ‘yan sandan su a hanya wajen tattara dukkan hujJojin su don shigar da ƙara a gaban Kotu.

Ya ce, amma a ‘yan sanda da EFCC ne kawai suke gudanar da binciken su, ba tare da ɗaukar ɗansanda mai gabatar da ƙara ba, inda hakan yasa ake samun giɓi wajen gudanar da bincike da lauya mai gabatar da ƙara ke amfani da damar sa.

Ya yi nuni da cewa, jama’ar gari suna son su san ƙa’idar da ake bi, domin kotu bata yin gaggawa kamar yadda suke tunani, sai dai kawai idan wanda ake tuhumar, ya amsa laifin da ake zargin sa dashi.

Tsohon Atoni ya bayyana cewa, ɗan sanda mai gabatar da ƙara, zai iya gatarwa da kotu ƙarar sa, har tsawon shekara amma kuma zuwan sa yin kariya a gaban kotun, his case for a year an ba a fara ba saboda yana da shedu da dama, haka shi kanshi Alƙalin, yana wasu ƙararraki a gabansa da yake aiki a kai.

Ya ce, dole ne sai mu yi haƙuri, domin akwai ƙa’idoji da dole sai an bisu, inda daga baya sai a samu sakamako mai kyau wajen yin hukunci akan ƙarar cin hanci da rashawa.

Ya kuma shawarci ƙwararru akan Shari’a dasu  dinga bin doka da oda, wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Shi ma da yake nashi jawabin a madadin Babban baƙo, Gwamna  Abiola Ajimobi na jahar  Oyo, ya yi kira ga ƙwararru akan Shari’a dasu dinga bin doka da oda wajen gudanar da aikin su.

Abiola wanda kwamishinan kuɗi da kasafi ya wakilce a wurin taron, Mista  Bimbo Adekanmbi, ya jaddada cewar dole ne ƙwararrun su sa ƙaimi wajen ganin ana bin dokar da oda, don su samu zarafin gano ƙwararrun da suke yiwa doka da oda karan tsaye.

Gwamnan ya ce, ƙwararrun suna da babbar rawa da zasu taka wajen ganin an rage annobar cin hanci da rashawa da kuma fito da martabar sana’ar su, musamman don don taimakawa wajen ciyar da tattalin arzikin ƙasar nan gaba.

Sabon shugaban ƙungiyar da aka zaɓa Yarima Ganiyu Adebayo, ya koka ne akan yadda wasu ƙwararru a ƙasar nan akan fannin Shari’a da ake samun su da cin hanci da rashawa.

A ƙarshe ya bada shawarar ga jihohi da ƙananan hukumomi da kamfanoni da ƙungiyoyin dasu kafa tsarin busa wusir akan masu cin cin hanci darashawa.

Exit mobile version