Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi: An Yi Kira Ga Al’umman Jihar Kano

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kan

Sakamakon kiran da hukumomin tsaro a jihar Kano su ka yi na buƙatar al’umma su haɗ a kai da jami’an tsaro wajen yaƙar matsalar shaye shayen miyagun kwaryoyi, al’ummar Garin Sheka da ke ƙaramar hukumar Kumbotso sun gudanar da taron masu ruwa da tsaki tare da kafa ƙungiyar sintiri domin kawo ƙarshen matsalar da ta addabi al’umma. Shugaban Kwamitin al’ummar wannan yanki na sheka Alhaji Kabiru Manawa ya jadadda buƙatar al’umma su fito domin haɗ a ƙarfi da jami’an tsaro wajen tsaftace baƙar ta’adar shaye shayen da ke adabar al’ummar Sheka.

Wannan kwamitin ya ƙunshi Matasa, dattijai, malamai da sauran masu ruwa da tsaki a wannan gari, kuma a cewarsa alhamdulillahi kwalliya ta biya kuɗ in sabulu, domin zuwa wannan lokaci an samu nasarar fatattakar  gungun mashaya da kuma dillalansu waɗ anda suka jima suna galabaitar da al’umma tare da hana su sakat. Cikin ayyukan da kwamitin ya gudanar akwai samame da aka kai gidan wani wanda ake zargi da safarar miyagun kayan maye musamman maganunuwan tari na ruwa, a lokacin farmakin an samu nasarar damƙe mutane tara ciki har da wata yarinya da iyayenta su ka ce rabonta da gida kwana 80.

Yanzu haka dai bayan doguwar tattaunawa an cimma daidaiton sayar da wannan gida domin tashi daga wannan unguwa, sannan kuma sauran waɗ anda aka damƙe tuni aka garzaya dasu gaban kulliya domin girbar abinda suka shuka. Idan ba’a manta kakakin runudunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya ya sha na na ta aniyar rundunar ‘yan sandan na yaƙi da masu sana’ar sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi, an jishi alokacin da al’ummar Hauren Mubi suka gudanar da irin wannan aikin sa aki, wanda Majiya ya tabbatar da cewar haka ya kamata ko wacce unguwa su ci gaba da tallafawa jami’an tsaro.

 

Exit mobile version