Idris Sulaiman Bala">

Ya A Ke Gane Mugu?

Mugunta ba a fuska ta ke ba, sannan ba a kowanne yanayi ba ne a ke gane fuskar mugu daga kallo. A wannan makon zan shiga bayani ne kan mugu da yadda a ke gane shi. saboda la’akari da yadda mugaye su ka mamaye mu a rayuwarmu ta yau da kullum.

Shi sannin mugu ya fi komi dadi, saboda idan ka san shi za ka san irin zaman da za ka yi da shi ta yadda ko da wasa ba za ka ba shi kafar da zai iya cutar da kai ba. domin shi mugu kiris ya ke jira ya yi illa.
A wasu lokuta za ka ji mutane na cewa, ‘Da ganin fuskarsa mugu ne’, wannan kawai zance ne. domin kuwa asalin mugu ba a iya gane shi ta fuska, karamin mugu ne a ke iya ganewa ta fuska har ma a iya ankarewa tare da daukan matakan da su ka dace.
kananan mugayen da a ke iya gane su ta fuska su ne wadanda ke cutar da mutum ta hanyar saane, kananan sace – sace, fyade, da sauransu. Idan ka shiga kasuwa, bisa la’akari da fuskokin wadanda ke kusa da kai, ka na iya gane mugu. Saboda siffar irin wadannan mugaye daban ta ke. Idan ka ga mutum ba ka yarda da shi ba, ka kura mishi ido, da kanshi zai kauce ya bar wurin don ya san ka gano mugu.
Irin wadannan kananan mugaye ba su son kallo ko kadan. Ko da cutar da mutum su ke son yi, idan ya cika tsura musu ido, su kan sha jinin jikinsu su bace.
kananan mugaye su kan tsinci kawunansu a harkar mugunta ne sakamakon wasu dalilai. Kadan daga ciki sun hada da rashin tawakkali, rashin wadatar zuci da kuma kyashi da sauransu. Amma wadannan su ne muhimman dalilan da ke jefa mutum ga sata da fyade.
A na gane babban mugu ta hanyoyi da dama, a cikin wadannan hanyoyi kuma akwai saukaka ta yadda ba sai ka tsaya wahalar da kanka ba. babban mugu shi ne wanda zai iya kashe ka, wanda burinshi shi ne ya ga ka lalace, wanda bai kaunar ci gabanka ko kadan, wanda bai son farin ciki a rayuwarka sai dai bakin ciki.
Mugu na da muguwar illa, shi rusa rayuwa ya ke yi. Duk ranar da mugu ya yi nasara a kan mutum, hakan na nufin mutum ya lalace kenan. Dalilin mugu ne a ke shawartan mutane da su shirya kansu, ma’ana su kasance masu tsarki da yawaitan addu’o’i.
Yawaita addu’o’i na taimakawa, amma ka gane wanene mugu shi ma ya na da muhimmancin gaske.
Mugu ya kan bat da kamanni ya bayyana a matsayin masoyi ko makusanci. Saboda ba kowanne mugu ba ne ke da karfin da zai iya bayyana ma ka kiyayya, wani zai rabe faran – faran cikin fara’a alhali a zuciyarshi ya na fatan faduwarka ne.
Ka lura da kyau, idan wani al’amarin murna ko karuwa ya same ka, duk yadda mugu ya kai ga danne zuciyarsa da yanayinshi da zaran ka kalli fuskarsa za ka ga ta canza ko da kuwa a dai dai lokacin ya na murmushi (yake) ne.
Idan ba ka iya gane shi ta fuska ba, ka natsu ka yi nazarin dukkanin kalaman da mutanen da ke wurin su ke fadi. Mugu ba zai yiwu ya yi magana tsaf ba, dole sai ya na yi ya na sarkewa, ko kuma ya na sakin layi.
Idan duk mutum bai iya yin amfani da wadancan dabaru ba, ga wata hanyar mai sauki. Matukar ka na da shakku a kan mutum, kuma ka na son sanin cewa mugu ne ko ba mugu ba. ka hada wani labari (ba na gaske ba) wanda idan labarin ya fita zai zama mai hatsari gare ka ko zai iya toshe ma hanyar arziki, sai ka fadi wa wannan mutum shi kadai.  Idan har wannan mutumin mugu ne, ba zai iya yin hakuri ba, dole sai ya fitar da labarin domin ka lalace.
Zai saki labarin ne tare da tunanin ai ba shi kadai ka fadi ma ba, ka ga wannan zai jefa mutum cikin tunanin to wanene ya fallasa. Amma idan mutum daya ne ya sani, ka ga babu wani tantama kenan.
Ka na iya kirkirar ma kanka mugu da kanka. Saboda matukar ka na yawan fankama a gaban mutane da nuna cewa ka fi su, dole ne a cikinsu sai zuciyar wani ta kitsa mishi mugunta da son ganin ka ruguzo zuwa matsayinsu ko don ka daina yi musu fankama da ji – ji da kai.
Babban mugu ya na fara mugunta ne sakamakon hassada da keta da son kai. Idan ka na hassada da wani, ba za ka taba ganin wani alheri a tattare da shi ba, sannan ba za ka so abin arziki ya same shi ba. mutumin da zuciyarshi ke da yawan keta, zai kasance babban mugu wanda burinshi sauran jama’a su yi ta wahala da fada wa kunci. Mutumin da ke tsananin son kanshi shi ma bai dauki mugunta a bakin komi ba, saboda matukar zai rasa, to zai iya aikata komi don kowa ma ya rasa.
Da yawan masu dabi’ar mugunta ciwon zuciya ne ke kashe su. Saboda za su kasance masu muradin ganin lalacewar mutum, idan kuma Allah ya dafawa wannan mutumin, sannan mutumin ya kiyaye tare da toshe kafofin da zai yiwu su cutar da shi, haka nan su na ji su na gani ya na habbaka, wannan ne ke bugun zuciyarsu. Allah ya tsare mu daga mugunta da mugu.

Mu hadu mako mai zuwa!

Exit mobile version