Khalid Idris Doya" />

Ya Auri Budurwarsa Bayan Ta Mutu Kan Sadaki 2,000 A Bauchi

Wani abu kamar almara ya faru a unguwar Abujan Kwara da ke cikin kwaryar Bauchi inda wani matashi mai suna Muhammad Salisu ya auri matacciyar budurwarsa mai suna Halima da suke zaune a unguwa daya a makon jiya.
Halima wacce ta rasu sakamakon gajeruwar rashin lafiyar da ta yi fama da shi. Bayan rasuwarta ne kuma aka daura mata aure da saurayinta da ta mace ta barci a wannan duniyar tare da alkawarin yin aure a tsakaninsu.
Auren ya dauru ne bayan da mutumin ya biya sadaki naira dubu biyu 2,000 ga iyalan mamaciyar budurwar tasa.
An nakalto cewa, marigayiyar budurwar ta taba shan alwashin cewa ita dai, ko bayan babu ranta, iyayenta su daura mata aure da Salisu (masoyinta).
Shi dai Salisu ya dauki tsawon lokaci yana soyayya da Halima wanda hakan ya kaisu ga yin alkawarin cewa ba za su taba rabuwa da juna ba har abada. Bayan jin dadi da ninkaya cikin kogin soyayya da suka yi na tsawon lokaci.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Malam Bahajatu Nasir, ma’aikaci a hukumar Shari’ar Musulunci ta jihar Bauchi, ya yi bayanin cewa, auren ya wakana ne a lokacin da mahaifiyar marigayiya Halima ta sanar da jama’a cewa an shirya jana’iza da bizne marigayiyar.
Ya ce, Malamin da ya jagoranci daura auren shine Malam Abubakar wanda kuma tunin hukumar Shari’ar Musulunci ta kama shi bisa aikata hakan.
Da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan wannan lamarin, wani Malamin addinin Islama a jihar Bauchi kuma Babban Limamin massallacin Jami’ar ATBU, Sheikh Mansur Isa Yalwa, ya misalta wannan auren a matsayin abun da bai dace ba kwata-kwata a addinin Musulunci.
A cewarsa, daga cikin matakan aure a Musulunci dole ne ma’auratan su kasance a raye, tare da karawa da cewa da zarar kuma daya daga cikinsu ya rasu, to zancen aure kuma ya kare.
“Don haka, ko auren ma da aka rigaya aka daura da zarar daya daga cikin ma’aurata biyu ya ko ta rasu, kai tsaye wannan auren ya rabu. Idan ta rasu, sai ka auri wata, in shine ya rasu sai ki auri wani. A batun da wani mutum ya auri wata matacciya, wannan auren ya saba wa koyarwar addinin Musulunci.”

Exit mobile version