Ya Dace Buhari Ya Sa Ido Kan Aikin Hanyar Abuja-Kano – Sakataren ‘Yan Lemo

Asibitoci

Isa Abdullahi Gidan ‘Bakko,

Ana ci gaba da nanata kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari day a kara sa ido na yadda ake yin aikin hanyar da ta taso daga Abuja zuwa Kano, domin kawo karshen rasa rayuka da ake yi dare da rana da kuma yadda ‘yan baya ga dangi ke aiwatar da muggan ayyuka da suka hada da garkuwa da mutane da fashi da makami da kuma kisar gilla da ke faruwa a wannan hanya,

Wannan kira ta fito ne daga bakin babban sakataren kungiyar ‘yan Lemo reshen kananan hukumomin Sabon gari da kuma Zariya Ustas Ahmad Dayyab Ya Salam,a lokacin day a amsa tambayoyin wakilinmu da ke Zariya.kan matsalolin da suke faruwa a wannan hanyar da aka ambata.

Ustas Ahmad Dayyab ya ci gaba da cewar, ga duk wanda ke mu’amala da wannan hanyar da ta taso daga Abuja zuwa Kaduna , a cewarsa , da zarar mutum ya fara tafiya daga Abuja zuwa Kaduna ko daga Abuja zuwa Kaduna ba shi da kwanciyar hankali sai fa mutum ya isa Abuja ko kuma isa garin Kaduna, kamar yadda ya ce a nan ne zai numfasa.

Sakataren ‘yan Lemon ya ci gaba da cewar, babu ko shakka, al’umma sun yi ittifakin cewar, lalacewar hanyar da kuma tafiyar hawainiya wajen gudanar da aikin da ake yi, su na kan gaba wajen yadda ma su garkuwa da mutane da ma su kisar gilla da kuma ‘yan fashi da makami suka mayar da hanyar a matsayin yadda suke cin karensu babu babbaka.

A cewarsa, lokaci ya yi da shugaban kasa da kansa zai sa ido a wannan hanya, tun da wadanda ya danka ma su amanar sa ido kan yadda ake yin aikin hanyar, alamu sun nuna ba sa bayyana ma sa gaskiyar matsalolin da suke faruwa a wannan hanya, da kowa ya yi amannar ta zama tarkon mutuwa ga wadanda bin hanyar dare da kuma rana.

Da kuma ya juya ga yadda lalacewar hanyar da kuma tafiyar hawainiya na yadda aikin ke tafiya, Ustas Ya Salam hya nunar da cewar, su da ke sana’ar Lemo, lalacewar hanyar ta shafe su na yadda, yadda motocin da suke dauko ma su Lemo daga kudancin Nijeriya zuwa arewa, su na shafe awanni ma su yawa, sabanin lokutan da suke dauka zuwa arewacin Nijeriya, kafin hanyar ta sami matsalolin da aka ambata.

Ya ci gaba da cewar, lokaci ya yi da  za a duba wannan hanya da al’umma za su sami sa’ida, tare da kawo karshen matsalolin da suke faruwa a hanyar na rasa rayuka da kisar gilla da kuma fashi da makami da ke faruwa a kan hanyar dare da kuma rana.

A karshe Ustas Ahmad Dayyab Ya Salam babban sakatare na kungiyar ‘yan Lemo a kananan hukumomim Zariya da Sabon gari, ya ce, maid a hankalin ganin an kammala wannan hanya, shi ne zai sa al’ummar arewa za su ce sun amfana da mulkin da ake yi ma su daga shekara ta 2015 zuwannan shekara ta 2021 da a ke ciki.

Exit mobile version