Wani matashi mai suna Kumar Marewad, dan shekara 17 daga garin Managundi da ke kasar Indiya, ya kasance mataccen da ya motsi bayan ya mutu. Amma wani abin mamaki shine, a likacin da duk danginsa suka tsaya a kan gawarsa, hawaye na bin fuskokinsu, bayan shirya gawar matashin, a yayin da suka shirin daukar Marewad zuwa makabarka. Mintuna kadan kafin farawar al’ada, dangin Kumar sun sami furgicin da basu taba samu ba a rayuwarsu, inda ba zato ba tsammani, kawai sai Kumar ya farka daga mutuwa.
Wani bataccen kare da ke kan titunan garin Karnataka ya ciji Kumar wata daya da ya gabata. Dabbobin da ba’a sansu ba sune tushen hadari a cikin Indiya. Shanu masu yawo da dare suna haifar da hadari. A sakamakon haka ne, wasu jihohin kasar ke fesa ruwan fenti mara illa a akan kahonnin shanon su. A wasu sassan kasar, dubban birai na yin sata daga shaguna suna afkawa mazauna yankin. A wani lamari, an taba samun wani biri mai ban tsoro da ya saci bas. Don haka, karnuka na iya zama babbar damuwa saboda kusancin su da mutane. A game da Marewad, ma’aikacin gini, cizon karen ya haifar masa da ‘meningoencephalitis’, wani cuta na mutuwa.
Bayan cizon karen, Marewad ya tafi asibitin gida. A can, ya sami magani daga Dr. Mahesh Neelakhantannabar. Amma duk da kokarin da likitan ya yi, halin da Kumar ke ciki ya ta’azzara. Da farko yana fama da kurji da zafi a duk ilahirinjikinsa, zazzabi da matsalolin numfashi da sauri suka biyo baya. Matsalolin numfashin ya ta’azzara wanda daga karshe sai ak sanya Kumar a tsarin tallafi na rayuwa, don samu iskar numfashi. Kwararrun likitocin sun gargadi dangin Marewad cewa zai yi huya Kumar ya murmure.
Duk da wasu shakku, da kuma gargadin kamuwa da cutar za ta yadu cikin sauri, likitocin sun sallami Kumar daga asibiti. Danginsa sun dauki matashin zuwa gida inda nan take ya mutu. Ko kuma, akalla ga dukkan alamu, ya mutu.