Connect with us

LABARAI

Ya Hallaka ’Yarsa Kwana Daya Kafin Aurenta A Anambra

Published

on

Wani magidanci mai shekaru sittin (60) da haihuwa mai suna Mr. Cletus Aguluka, ana zarginsa da kashe ‘yarsa mai suna Miss Onyinye Aguluka, a lokacin da take tsada da barci.

Rahoton da ya zo mana, tuni aka tsara a bisa al’ada za a yi wa Onyinye Aguluka aure a jiha Asabar, inda kuma mahaifinta ya yankata har lahira kwana gudana kafin a daura mata aure.

Wannan mummunar abun takaici da ban haushi dai ya auku ne da misalin karfe biyu na safiyar ranar Juma’a a Osikwu da ke kauyen Awgbu a yankin Orumba ta Arewa da ke jihar Anambra.

Kamar yadda matar wanda ake zargin da take bayani, Mrs. Georgina Aguluka, ta shaida cewar matsalar ta fara tasowa ne daidai lokacin da mai gidan nata ya dawo gida tsakar dare, inda ya nemi na’urar hasken wutar lantarki ya rasa.

“’Yaransa sun fada masa cewar ba su san inda abun da yake nema yake ba. Daga nan ne kawai ya dai tashi da misalin karfe daya na safiya, ya shiga cikin dakinsa, fitowarsa kawai sai ya dauko wuka ya daba wa ‘yarsa,”

Wani kanin wanda ake zargin ya shaida cewar dan uwansa mutum ne mai masifar tsauwala wa jama’a, musamman iyalan gidansa ciki kuwa har da shi kansa kanin nasa, ya bayyana cewar dan uwansa mutum ne mai matukar tsananin gaske, ya kuma shaida cewar yayansa na da tsatstsauran ra’ayi kan lamari.

Ganau sun shaida cewar wanda ya aikata laifin ya arci na kare bayan da ya aikata aika-aikar tasa, inda kuma ‘yan banga suka hanzarta zuwa gidan hade da daukan gawan mamaciyar zuwa inda ta dace.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra SP Haruna Muhammad ya tabbatar da aukuwar lamarin wa ‘yan jarida a Awka, inda ya shaida cewar tuni suka sankamo wanda suke zargi da aikata lamarin.

Sifiritandan Haruna Muhammad ya ce “Haka ne, tabbas lamarin ta auku ne a ranar 31 ga watan Mayu na shekara ta 2018 wajajen karfe biyu na safiya. Mun samu nasarar kame wanda ake zargi a ranar 1 ga watan June (kwana guda da kisan da ya yi).

SP ya bayyana cewar har zuwa yanzu suna kan ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin suna kuma kammalawa za su gurfanar da shi a gaban kuliya domin fuskantar shari’a.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: