Ya Harbi Mata 30 Da Cutar Ƙanjamau

Daga Bello Hamza

Wani mai ɗauke da cutar Ƙanjamau da ya harbi mata fiye da 30 a cikin shekara 10 da ya yi yana lalata da su ba tare da kariya ba, zai fuskanci hukuncin ɗaurin rai-da-rai a gidan yari.

Rebibbia ɗan shekara 33 ya yaudari yawancin matan ne ta kafafen sadarwa na zamani (social networks and internet dating sites), cikin mata 53 da aka gano ya yi lalata da su tsakain shekarar 2006 zuwa 2015 binciken ya nuna cewa, mata 33 tuni suka kamu da cutar Ƙanjamau, cuta mai karya garkuwar jikin ɗan’adam. Uku daga cikin samarin waɗannan matan su ma sun kamu haka kuma ɗan daya daga cikinsu.

A shari’ar da aka gudanar a gidan yarin Rebibbia da ke ƙasar Rum, matan sun bada shaidar yadda Talluto ya yaudare su ta hanyar yin jima’i da su, ba tare da kariya ba. Sun bayyana cewa, duk lokacin da suka buƙaci ya sa kwaroron roba sai ya ce “kwanannan na yi gwajin cutar Ƙanjamau, lafiyata lau”

Lokacin da suka gano cewa sun kamu da cutar Ƙanjamau bayan rashin lafiyar da ya addabe su da kuma gwaji da suka yi, sun tuntuɓe shi amma ya nuna cewa, ba abin da ya shafe shi.

Binciken, ya nuna cewa ma fi ƙarancin shekaru cikin matan ita ce ‘yar shekara 14, yayin da ‘yar shekara 40 ce ma fi tsufa, kuma yakan yi hulɗa da mata fiye da 6 a lokaci ɗaya, daga baya ya kora su bayan ya harbe su da ƙwayar cutar. Kowace ta bayyana wa kotu irin halin da ta shiga sakamakon wannan cutar.

Masu gabatar da ƙara dai na neman kotu da ta yanke wa Rebibbia hukuncin ɗaurin rai-da-rai sakamako sa rayuwar waɗannan mata cikin mugun hali.

Exit mobile version