Mahdi M Muhammad" />

Ya Tsunduma Motarsa Cikin Kogi Yayin Da Yake Bin Umarnin ‘Google Map’

‘Google Map’

Wani ba indiye ya nitse bayan ya jefa motarsa a cikin wata madatsar ruwa yayin da ake zargin yana bin umarnin ‘Google Maps Nabigation’.

A cewar rahoton na kamfanin ‘Indian Edpress’, Satish Ghule, mai shekara 34, yana tuka mai gidansa Guru Shekhar, mai shekara 42, da abokinsa Sameer Rajurkar, mai shekara 44, a ranar Lahadi a garin Akole, gundumar Ahmednagar da ke jihar Maharashtra. Ma’aikatan ukun da za je batun wani aiki ne a Kalsubai, mafi girman tsawan Maharashtra.

Yayin tuki zuwa Kalsubai, sun bace hanya kuma sun nemi kwatance daga ‘Google Maps’. Kwatancen ya nuna musu wata hanyar da ta hada da wata gada wacce ta kasance a karkashin ruwa na kimanin watanni 4 bayan da hukumomi suka saki ruwan daga madatsar ruwan Pimpalgaon. Haka zalika, ba a sabunta bayanin a kan Taswirorin ‘Google’ ba saboda haka babu wani gargadi a kan taswirar, ‘Cartok’.

Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda Rahul Madhne ya ce, “Akwai wata gada a can, wacce ke aiki tsawon watanni takwas. Amma tsawon watanni hudu bayan damina, ana sakin ruwan dam din kuma gadar tana shiga karkashin ruwa, saboda haka ba za a iya amfani da ita ba.”

Kasancewar da dare ne, ma’aikatan sun fada cikin madatsar ruwan ne ba basu sani ba. Basu lura ba a lokacin da suka afka cikin ruwan. A cewar ‘yan sanda, mutum ukun sun samu nasarar fitowa bayan sun bude tagar motar. Amma Ghule, direban motar, wanda bai san yadda ake iyo ba, ya kasa ceton kansa yayin da Shekhar da Rajurkar suka yi iyo suka zo bakin tekun.

Cikin Ghule ya cika da ruwa da safiyar Lahadi, a inda aka garzaya da shi zuwa wani wurin kula da lafiyar jama’a da ke kusa, inda aka bayyana cewa ya mutu a lokacin da aka isa wurin. ‘Yan sanda sun ce sun yi rajistar lamarin a matsayin mutuwar bazata.

Exit mobile version