Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Ya Kamata A Ba Da Muhimmanci Ga Raya Noma Da Kyautata Amfani Da Albarkatun Ruwa

Published

on

A ranar Talata 9 ga watan nan ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci birnin Yinchuan dake jihar Ningxia mai cin gashin kanta ta kabilar Hui dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Yayin wannan ziyara, shugaba Xi ya leka lambun kare halittu na yawon bude ido dake kusa da tsaunin Helan, don ganewa idanun sa irin ci gaba da aka samu, a fannin raya ayyukan noma, da kuma irin kokari da ake yi na karfafa matakan kare muhallin halittun dake tsaunin na Helan. Kaza lika ya jaddada muhimmancin amfani da salon noma mai kunshe da dabarun kyautata amfani da ruwa, tare da aiwatar da matakan dakile barnata ruwa yayin noman rani, lokacin da ya ziyarci wasu filayen noma dake yankin.
Shugaba Xi ya kuma ba da shawarar kyautata dabaru, ta yadda za a kai ga kare moriya daga ruwa. Yana mai cewa, alummar Ningxia sun yi dacen makwaftaka da kogin Yellow River mai kunshe da albarkatun ruwa da dama.
Wannan ne dai karo na hudu da shugaba Xi ke ziyartar yankin wannan muhimmin kogi, wanda ya bayyana kare shi a matsayin muhimmin aiki da zai taimaka wajen farfadowa, da wanzar da ci gaban kasar Sin.
Masu iya magana dai kan ce “noma tushen arziki, kuma bawan damana shi ne attajirin rani”. Wannan ya sa a har kullum, shugaban na Sin ke dora muhimmancin gaske ga dukkanin wasu ayyuka masu nasaba da raya harkar noma.
Sanin kowa ne noma a wannan zamani ya wuce batun shuka yabanya a lokutan damuna kadai, a yanzu harkar noma ta kunshi dabaru daban daban da ake amfani da su wajen kyautata samar da tsirrai, da inganta filayen noma, da dabarun takaita amfani da ruwa, da managartan dabaru na kare amfani daga kwari, da sauran matsaloli yayin da ake noma amfanin gona.
A hannu guda kuma kyautata ajiyar yabanya, da kara daga darajarta a kasuwanni, tare da kare manoma daga fadawa cikin hasara, su ma muhimman fannoni ne dake bunkasa wannan tsohuwar sana’a, wadda ke matsayin kashin bayan ci gaban rayuwar bil Adama.
Idan mun yi duba a tsanaki cikin kalaman shugaba Xi yayin wannan ziyara ta baya bayan nan, za mu ga yadda ya jaddada muhimmancin amfani da ruwa ta hanyoyi mafiya dace, da kaucewa barnata ruwa a lokacin da ake noman rani. Hakika wannan batu yana da matukar muhimmanci, ganin cewa, baya ga amfani da ruwa a filayen noma, a hannu guda al’umma na kuma bukatar ruwa domin harkokin rayuwa na yau da kullum, kamar sha, da tsaftar jiki da ta muhalli, da sarrafa nau’o’in hajoji daban daban, kuma wannan bukata ba za ta biya ba, muddin ba a dora muhimmanci wajen kawar da barnata ruwa ba.
Bangaren kare muhallin halittu da tsaunuka shi ma yana taka rawa matuka, a fannin kyautata yanayin zaman rayuwar al’umma, a fannin kyautata iskar da bil Adama ke shaka, da rage gurbatar iska, da dorewar rayuwar halittu daban daban dake a gandayen daji.
Ko shakka babu, idan mun kalli wadannan fannoni da kyau, za mu dada fahimtar ingancin salon jagorancin shugaba Xi Jinping, da ma JKS, ta yadda har kullum suke tsaiwa tsayin daka wajen tsara kyawawan manufofi na ingantawa da kare daukacin sassan rayuwar bil Adama ba tare da kasala ba.
Fatanmu shi ne ragowar sassan duniya, za su rika koyi da irin wadannan dabaru, wadanda ko shakka babu, na iya magance kalubaloli da dama da duniyar bil Adama ke fuskanta a irin wannan lokaci mai cike da sauye sauye. (Marubuci: Saminu Hassan daga CRI Hausa)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: