Ya Kamata A Ba Wa Matasa Dama A Harkar Siyasa – Ishak Idris

Harkar Siyasa

HON. ISHAK IDRIS matashi ne a majalisar matasa ta kasa kuma dan siyasa a cikin matasan karamar hukumar Sabon Gari, ya bayyana wa al’umma ra’ayinsa yayin zantawarsu da Wakilin LEADERSHIP A YAU, IDRIS UMAR ZARIYA. Ga yadda zantawar tasu ta kasance:

 

Ranka ya dade masu karatu za su so su ji sunanka da matsayinka a wannan karamar hukuma ta Sabon Gari?

Assalamu alaikum, sunana Ishak Idris, kuma nine wakilin Sabon Gari a majalisar matasa ta jihar Kaduna, Youth Council of Nigeria. Kuma nine mataimakin shugaban majalisar matasa ta Sabon Gari Local Gobernment, kuma ina daya daga cikin shugabannin jam’iyyar APC a yankin Bomo, abinda zan iya bayarwa kenan..

 

To ranka ya dade kasantuwan duk abinda za a yi a wannan kasar kashin bayansa matasa ne, yanzu a daidai wannan lokacin an fara kada gangar siyasa a wannan karamar hukuma ta Sabon Gari, ta inda wasu ke bayar da shawarwari a matsayinka na daya daga cikin wadanda suka san abinda ke faruwa a karamar hukumar Sabon Gari, wace shawara za ka ba matasa a siyasance wadda za ta taimaka masu wajen fitar da wadanda za su taimakawa rayuwar matasa a wannan lokacin?

To alhamdulillahi, lokaci ne na siyasa wanda Nijeriya na bukatar jajurtattun ‘yan siyasa kuma atleast a ce matasa ne domin su suke da jini a jika, to ko don a samu ingantaccen shugabanci ana bukatar idan ka fita sai ka dawo, idan ka fita ka yi aiki da lafiyar da Allah Ya hore maka a matsayinka na matashi, kuma matashi ne yanzu zai yi maka tunani cikin minti biyu, tunaninshi ta kai inda ba ka yi tunani ba. To gaskiya ya kamata mu maida hankali, a zabo matasa masu hankali domin su nemi wannan shugabanci, yanzu misali kamar Sabon Gari Local gobernment inda na ke wakilta, a gaskiya shugaban karamar hukumar Sabon Gari ya janyo matasa a cikin harkokinsa musamman Youth Council duk abinda ya zo karamar hukuma na taimakawa yana ba matasa slots, saboda muhimmancinsu to wannan ya na sake grooming dinsu ne saboda idan lokaci ya zo su samu damar da za su iya yin shugabanci. Saboda haka ni ina bada shawarar matasa su fito su nemi shugabanci ko dan wannan security problem da muke da shi a Nijeriya, idan suka nemi shugabanci sun amfanin ‘yan uwansu matasa za su dan janyo su a jiki domin su samar masu da abin yi domin rage matsalolin da ake samu a kasa.

 

To ranka ya dade in za ka ba gwamnati shawara, tsayuwa da aiki na alkairi sai an koya wa mutum, wace shawara za ka bayar ga gwamnati dangane da hanyar da za ta bayar ko kuma ta gwadawa matashi sanin muhimmancin kansa?

To, da ma ni bangaren karatuna ne hulda da jama’a, musamman na yi digiri na na farko a Public Administration, na yi digiri na biyu a Piblicn.Public Administration, yanzu ina yin digiri na uku a Public Administration, to saboda haka abu ne kalilan za a yi, matasan nan an san su, an san sun rabu kala-kala, akwai wanda sun bi hanya mara kyau, akwai wanda shaye-shaye ne, akwai wanda sun gama karatun sun sami aiki. To shuwagabannin kungiyoyi na kowanne yanki wallahi sun san wadannan mutanen. A janyo kungiyoyi kusa da gwamnati, su sun san wadannan mutanen, kamar mu yanzu a cikin tsari na siyasa abinda mu ke hangowa muke so mu ba gwamnati shawara ko kuma idan Allah Ya bamu dama in mun shiga gwamnati abinda muke so mu ba gwamnati shawara, kungiyoyin da suke kowanne yanki a basu muhimmanci indai sun yi register, kamar ni yanzu na yiwa kungiyoyi 32 register da kudina a kan a zamar da su a gwamnatance, saboda idan gwamnati ta tashi kiran kungiyoyi tana kiran wadanda suka yi register ne, sai su fadi matsalolin da ke damunsu, gwamnati za ta sairaresu za su fadi wannan koke nasu, to gwamnati za ta dauki gaggawa. Ta zauna da su ta sauraresu koda karamar hukuma ne ko jiha ne, su suka san bata gari, su suka san masu shaye-shaye, su suka san mutanen kirki, to motibating din su ba zai yi wahala ba. A janyo su a kawo su kusa da gwamnati insha Allahu ba za a samu matsala ba wajen control na abin, to shine shawarata.

 

To ban sani ba ko wace shawara za ka ba wa su matasa musamman a harka ta shaye-shaye, idan gwamnati ba ta dau mataki ba shin za ka cigaba da shaye-shayen ne? Ko akwai wani mataki da ku a matsayinku na masana musamman a matsayinku na shuwagabannin kungiyoyi akwai wata shawara da za ku iya ba matasa a kan wannan lamari?

Akwai matakan da muke dauka, akwai lokacin da musamman kamar su majisar matasa ta Sabon Gari Local Gobernment akwai lokacin da suka tsintsinto wasu daga cikin masu shaye-shaye, to wannan musamman aka zo aka dan basu training aka kuma fadi illar shaye-shaye, na biyu akwai lokacin da muka yi inbiting kamar karuwai masu zaman kansu muka nuna masu illar wannan karuwanci da suke yi, sannan ni kamar a yanki na na Bomo a unguwata ta Hayin Dogo, akwai training center da muka hada karkashin jagorancin Malam Abdullahi Jafar, malam A.G, zai tattara akwai wata farfesa a ABU da take kawo mana support, muna zama da su gaskiya fisabilillahi mun ci nasara, dan ni akwai wajen guda biyar da suke zuwa mun hira tun wajen magariba sai isha’i suke tashi, daidai lokacin suke zuwa shaye-shayen, to wasu kuma mun janyo su sun koma makaranta. To kuma guda biyu a ciki sun sami admission a nan jami’ar Ahmadu Bello, da za a karawa abin karfi to da atleast an rage kaifin abubuwan, tunda ni ka ga na tsaya a Hayin Dogo ne da ina da power da zan iya shiga Bomo, Kurmin Bomo, Kwakwaren Manu, inda duk za ka iske wadannan matsalolin, to a hankali dai muna fadawa gwamnati. Rubutun da na yi sati biyu da suka wuce na rubuta cewa ina kira ga gwamnati da take kula da kungoyoyi, domin kumgiyoyi su suka san halin da ake ciki a kasa, in ka ji kungiya to sarki ya yarda da ita to indai ana kula da su to za a samu control a kan yanayin shaye-shayen sannan kuma su matasa muna janyo su a jiki ne domin in sun saki layi sai a hankali, muna basu shawara a je a yi karatu, shekarunku sun kai da in ka rike sana’arka ya kamata a ce kana da yaro zai ce gaskiya ne. Mu janyo hankalinsu muna yi masu alkairi, mukan ce ku je ku yi sana’a, to inda abin ke kakare mana sai kakabashi to wadansu mukan.dan yi na iya kasa wasu kuma gaskiya bamu iyawa, to a haka dai muke dan janyo hankali kuma in Allah Ya yarda akwai nasara.

 

To Kwamret ban sani ba a karshe ban sani ba me mutum ya kamata ya tanadarwa kanshi sa’ilin da ya ke so ya fada cikin siyasa?

To alhamdulillahi shi dai siyasa wani abu ne da abinda ka shuka shi ka ke girbewa. Ana nan ana kula da harkokinka, ana nan ana bibiyarka, to gaskiya damar da muka samu da mu kanmu da ‘yan uwanmu matasa, to ba abinda ya ke biyo baya sai tarihi me ka yi? Na shiga majalisar matasa ni don al’umma na shiga majalisar matasa, ba a biyana albashi ko alawus amma akwai wasu damammaki a cikin ta, Allah kadai ya san iyakar damammakin amma babu albashi a cikinta. To a cikin wannan damammakin da nake samu za ka ga mutane sun zo sun kawo complain, a wannan damar na majalisar matasa za ka yi solbing problems din, a majalisar matasa na ke samun opportunity na ke yin registration na kungiyoyi. Kungoyoyin nan akalla kusan talatin akwai a Kurmi, akwai a Bomo, akwai a Hayin Dogo, cikin Samaru duk nine na yi musu registration, wannan zai iya yi mana shugabanci, a majalisar matasa akwai wadanda basu da lafiya muryar mu yana tafiya za mu dauka mu kai asibiti, a majalisar matasa akwai programmes da muke shiryawa da yawa kamar wasan kwallon kafa da muke shiryawa, to akwai programmes da mu ke shiryawa da ake tunanin irinmu idan aka bamu dama a gwamnati za mu iya yin aiki kan jiki kan karfi ya fi wanda suke kai a yanzu, to irin wannan opportunity ba kai ne za ka ce zan yi siyasa ba, su matasa harda dattawa ma, don kamar tafiyarmu da muka fara tsarawa za ka ga kowa da kowa ne yana fatan mu zo mu yi mukami kaza, to ka ga wannan ba karamin cigaba bane, ka ga kamar yanki na na Bomo ban furta ba amma kiran da ake min a social media na in fito takara wallahi ko furtawa na yi ba zan kai haka ba da wajen taro da wajen taron siyasa ba mamaki ta yiwu lokaci ya zo da a gwamnatance zan bayar da gudummuwa na, shi ya sa na ke jawo hankalin ‘yan uwana wadanda suka samu dama a siyasa da su yi aiki da kyakkyawar niyya da kyakkyawar zuciya fatan cewa wannan damar ta zame masu alheri, domin Allah ne kadai Ya sani da haka ya ke faruwa.

Exit mobile version