Connect with us

WASANNI

Ya Kamata A Cigaba Da Goya Wa Mourinho Baya, In Ji Giggs

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ryan Giggs, ya bayyana cewa yakamata magoya bayan kungiyar suci gaba da goyawa kociyan kungiyar baya domin ya fitar da kungiyar daga halin da take ciki a yanzu.

Mourinho dai yana cikin halin kunci a kungiyar tun farkon fara shirye shiryen kakar wannan shekarar bayan day a zargi shugaban kungiyar da kin siyo masa dan wasan baya wanda yace yana bukata domin kara karfi a baya.

Manchester United dai ta buga wasanni uku a gasar firimiya sai dai tayi rashin nasara a wasanni biyu sannan kuma tayi nasara a wasan farko data buga hakan yasa ake ganin kamar kungiyar zata iya korar kociyan nata.

Sai dai tsohon dan wasa Giggs ya  bayyana cewa wannan ne lokacin da yakamata magoya baya su goyi bayan kungiyar da kuma mai koyar da ita saboda idan yasamu goyon bayansu zai fitar da kungiyar daga halin da take ciki.

“A yanzu yakamata a goyawa Mourinho baya saboda shine yasan asalin matsalar da take damun kungiyar kuma shine kadai zai iya fitar da ita daga ciki saboda yasan aikin yadda yakamata” in ji Giggs, wanda ya taba zama kociyan kungiyar na rikon kwarya na tsawon wasanni hudu lokacin da aka kori Dabid Moyes.

Yaci gaba da cewa ‘Ina filin wasan a ranar Litinin da suka sha kashi a hannun Tottenham kuma ‘yan wasa sunyi kokari yadda yakamata amma kuma daman kungiyar takan shiga irin wadannan matsalolo kuma ta fita lafiya”

A karshe kuma Giggs ya bayyana cewa baya neman zama kociyan kungiyar a yanzu saboda yana tare da tawagar ‘yan wasan kasar Wales a matsayin mai koyarwa.
Advertisement

labarai