Ya Kamata A Fara Amfani Da ‘Yan Bautar Kasa Wajen Yaki Da ‘Yan Bindiga – Gwamna Fayemi  

Fayemi

Daga Yusuf Shuaibu,

Gwamnan Jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da sassanin bautar (NYSC) zuwa wajen horar da ‘yan bautan kasa, domin su taimaka wa sojoji da ‘yan sanda wajen samar da tsaro.

 

Mista Fayemi ya bayyana cewa daya daga cikin hanyoyin da za a samu nasarar aiwatar da lamarin shi ne a sauya dokar NYSC.

 

“Da wannan ne za mu sami damar yin amfani da sassanin ‘yan bautar kasa wajen horar da daliban da suka kammala digiri ta yadda za su taimaka wa jami’an tsaro karkashin tsari na musamman. Ta wannan hanyar, za a ware wasu kudade tsakanin shekaru biyar zuwa 10 wajen ganin an cimma wannan lamari. Sannan wadanda suke bukatar shiga aikin soja daga cikin ‘yan bautar kasar sai su ci gaba ba tare da wani wahala ba.”

 

A watan Yuni, Darakta Janar na NYSC, Shuaibu Ibrahim ya bayyana cewa ‘yan bautar kasa sun cancanci zuwa yaki, domin suna cikin wani bangare na tsarin tsaron Nijeriya wanda ya kamata a tura su yaki.

 

Mista Fayemi ya kara bayyana cewa wannan mataki yana da matukar muhimmanci, domin cikin sauki za a samu jami’an tsaro guda 200,000 wanda Nijeriya ke bukata wajen magance tsaro.

 

“Kidiggata ya nuna cewa, akalla muna bukatar jami’an tsaro da suka kai 200,000 wajen yakir rashin tsaro a kasar nan,” in ji Gwamnan Ekiti.

 

A cikin watan Yuli, Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku ya yi irin wannan tunani wanda ya bukaci a samar wa NYSC wani shiri na shekaru biyu da zai bayar da horon sojoji ga masu bautar kasa.

 

Mista Fayemi ya bayyana hakan ne a garin Ibadan lokacin da yake jawabi wajen murnar ranar haihuwar Babatunde Oduyoye, wanda shi ne mai bai wa Gwamna Seyi Makinde shawara a bangaren harkokin siyasa. Shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya ya kara da cewa babu wani abun da ya fi damun ‘yan Nijeriya face matsalar tsaro wanda shi ne babban batu da ke damun kasar nan.

 

Ya kara jaddada cewa akwai bukatar samun karin jami’an tsaro wadanda za su magance matsalar tsaro a Nijeriya. Mista Fayemi ya yi kira ga shugabanni da su hada kai wajen tunkarar ‘yan ta’adda wadanda ba sa mutunta yara, tsofaffi, mata, shugabannin addinai ko kuma sarakuna.

Exit mobile version