CRI Hausa" />

Ya Kamata A Gina Tsarin Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ga Dukkan Bil Adama

“Ya kamata a tabbatar da hadin gwiwar bangarori daban daban a duniya” “Ya kamata a gina tsarin al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama”

Wadannan wasu kalamai ne wadanda a mafi yawan lokuta shugaba Xi Jinping yake yawan maimaita su a wuraren tarukan kolin kasa da kasa.
Kwanaki kadan da suka shude, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya sanar cewa, shugaban zai amsa goron gayyatar halartar babban taron cika shekaru 75 da kafuwar MDD, kuma zai gabatar da muhimmin jawabi ta kafar bidiyo. Koda yake, a shekaru da dama, shugaba Xi Jinping ya sha fayyace bayanai game da manufar gina tsarin al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama a lokutan da yake halartar manyan tarukan kasa da kasa, inda ya sha nanatawa duniya cewa, al’ummar Sinawa suna da muradin yin aiki tare da jama’ar dukkan kasashen duniya domin a gina ingantaccen muhallin rayuwa ga daukacin al’ummar duniya. Alal misali, a lokacin da ya halarci muhawara a babban taron MDD karo na 70 a shekarar 2015, shugaba Xi Jinping ya sha nanata cewa zaman lafiya, ci gaba, adalci, demokaradiyya, da ’yanci, su ne muhimman ginshikan dake shafar daukacin bil adama kuma su ne manyan kudurorin MDD. A duniyar da muke a yau, dukkannin kasashen duniya suna damfare da junansu ne, suna musayar dadi da wuya tare. Ya kamata dukkan bangarori su rungumi tsare-tsaren manufofin MDD, su yi kokarin gina sabon tsarin huldar kasa da kasa mai cike da manufar cin moriyar juna, kuma a yi kokarin gina tsarin al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama. Shekaru biyu daga bisani, shugaba Xi ya gabatar da muhimmin jawabi mai taken, “Mu hada gwiwar gina tsarin al’umma mai kyakkyawar makoma ga bil adama” wanda ya gabatar a helkwatar MDD dake birnin Geneva. Haka zalika, ya taba jaddada cewa, “Ya kamata kasashen duniya su gina tsarin hadin gwiwar tattaunawa, ba tare da yin fito-na-fito ba, kuma su yi hulda da juna ba tayar da jijiyar wuya ba. Ya kamata manyan kasashe su girmama muhimman bukatu da moriyar junansu, su magance rikice-rikice, da kawar da banbance banbance a tsakaninsu, su sa himma da kwazo wajen gina sabuwar duniya mai cike da zaman lafiya, ba tare da tsokanar juna ba, su girmama juna, da kulla dangantakar moriya ga kowane bangare.”
Xi Jinping ya sha nanata cewa, tilas ne a samar da yanayin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa, a yi musayar damammaki da moriya mai salon bude kofa, kuma a yi kokarin cimma nasarar kafa tsarin hadin gwiwa wanda zai samar da sakamako na moriyar juna.
A cikin jawabin da ya gabatar a taron bikin cika shekaru 75 da kafuwar MDD ta kafar bidyo, shugaba Xi Jinping ya ce, wajibi ne MDD ta kasance mai nuna adalci, da martaba doka, da bunkasa alakar kasancewar bangarori daban-daban, da mayar da hankali kan matakan da suka dace a dauka domin ganin bayan annobar COVID-19. Ya kuma nanata kudirin kasar Sin na kasancewar bangarori daban-daban, da yin gyare-gyare da bunkasa tsarin tafiyar da harkokin duniya, tare da alkawarin gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama. Tabbas jawabin na shugaba Xi ya samu yabo daga masana na ketare, babban sakataren MDD, Antonio Guterres da babban darektan hukumar kula da kaurar jama’a ta duniya, duk sun bayyana cewa, kalaman shugaba Xi game da kudirin kasarsa na nacewa ga kasancewar bangarori daban-daban kan harkokin kasa da kasa, wata alama ce a fili dake nuna babbar rawar da tsarin MDD yake takawa, na kasancewa tare da goyon bayan kasashe mambobin majalisar, a wannan lokaci da duniya ke fama da wannan annoba. Shi ma darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya, Charles Onunaiju, ya bayyana cewa, kasar Sin ta fito da wata taswira a zahiri dake bayyana bukatar gina al’umma ta bai daya, ta hanyar amfani da shawarar nan ta “Ziri daya da hanya daya”, don kafa tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa ba tare da wata rufa-rufa ba. Ko shakka babu, yabon gwani ya zama dole. (Ahmad Fagam)

Exit mobile version