Ya Kamata A Rika Yi Wa Mata Alkawarin Siyasa A Rubuce – Hajiya Zarah

HAJIYA ZARAH ABDULLAHI, ita ce shugabar gidauniyar Zarah and Author kuma cikakkiyar ‘yar siyasa, a tattaunawarta da wakilinmu MUHAMMAD AWWAL UMAR, ta ce ‘yan siyasa na ci da gumin mata, wanda dole a sake lale wajen tafiyar neman mulki. Har ila yau ta yo tsokaci kan matsalar tasaro a kasar tare da bayar da shawara: Ga dai hirar:

 

Ranki ya dade a kwanakin baya Majalisar dinkin Duniya ta yi bikin ranar mata ta duniya inda masana suka tattauna matsalolin mata da dama. Idan mun koma bangaren siyasa da mulki wasu abubuwa ne kika hango suna danne hakkin mata?

Da farko muna godiya ga Allah bisa nagarta da jajircewar mu iyaye mata, tabbas masana da dama sun tattauna a kafafen yada labarai akan matsalolin da mata ke fuskanta duk da cewar sune kashin bayan cigaban kowace al’umma.

Yau muna maganar siyasa da gudunmawar mata a tafiyar da mulki daga matakan kananan hukumomi zuwa jahohi har kan tarayya, sau tari za ka ci gwamnatoci da dama suna fadin sun baiwa mata damar taka rawa amma idan aka yi nazari da hangen nesa duk kurarin da za ka ji ana yi ba a baiwa mata kashi ashirin balle talatin da biyar da majalisar dunkin duniya ta ayyana.

Wannan matakin bai rasa nasaba da rashin daukar matan da muhimmanci sai a lokacin zabe ko ana neman kuri’a domin an san kashi saba’in da biyar da ake samu na kuri’a a lokacin zabe daga mata yake fitowa. Saboda mu mata muna da alkawari, a duk lokacin da mace daya tace za tai abu ko tana goyon bayan jam’iyya ko dan takara a dalilin kuri’ar mace daya tana iya jawo a samu kuri’a sama sittin, amma mai makon idan an kai ga nasara sai ka ga a lokacin da za a bijiro da maganar mace ba ta shugabanci, wani lokacin koda matan sun tsaya kai da fata sai ka tarar ha ilau kujerun da za a ba su na je ka na yi ka ne ba wani yunkurin kirki za ta iya yi balle ta taka rawar da ya dace.

Amma ba kya ganin hakan bai rasa nasaba da tsayin dakan ku mata wajen ganin kun samu matsayin da ya kamata?

Ba haka ba ne, ai lokacin da ake shirya tafiyar mu ake sanyawa a gaba amma da zaran an cin ma romon ne ake mayar da mu baya. A lokacin maganar wakilci ke tasowa, a lokacin ne ake nuna cewar muna da rauni da makamantan su, wanda ka ga bai dace a zarge mu ba. Da ina duba wahalar mutum da irin gudunmawar da ya bayar a tafiya da ba a rika cin duddugen mu ba.

 

Idan na fahimce ki kamar kina nufin ana ci da gumin ku ne mata a tafiyar da siyasa da shugabanci.

kwarai haka ne, domin akan yi karfa karfa a baza mana manyan riguna a danne wanda hakan kuwa ba a dalci ba ne. Kan haka ne gidauniyar mu ta Zarah and Author ta tashi haikan wajen wayar da kan mata musamman ganin irin gudunmawar da suke bayarwa dan a daina mayar da su baya, zuwa yanzu wasu jahohin sun dan tabuka amma akwai bukatar su din ma su kara kaimi musamman jahohin arewa.

Yau kamar yadda muka ga Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru el-Rufa’i ya dauko mace ta zama mataimakiyar gwamna a arewa, nan gaba a samu wasu jahohin su yi koyi da shi, in ma ta kama mu ga an bai wa mace dama ta zama gwamna a lokacin ne za mu yarda cewar an daina danne mu, an daina tauye mana hakki.

Da za ki ba da shawara, wace shawara za ki baiwa ‘yan uwanki mata a kan tafiyar siyasa da mulki?

Mu kafa kungiya mai karfi da za ta sanya idanu, mu rika magana da murya daya. Duk lokacin da za a yi tafiyar siyasa in har za a sanya mata to mu yi alkawari a rubuce idan an kai ga nasara a tabbatar da alkawarin nan. Ya zama mun fita daga sahun ‘yan amshin shata, muna da damar rike kowace irin kujera, muna da mata hazikai nagartattu masu kuzarin da za su iya taka duk wata rawar da maza takawa, domin saboda amanar mace a kasar nan kafin ka ji an kama mace daya da laifin rashawa daya an samu maza goma. Mu iyaye ne, mu ke baiwa al’umma tarbiya to wannan na nuna cewar idan muka samu shugabanci za mu rike amanar da aka ba mu da gaskiya.

 

Arewacin kasar nan na fama da matsalar tsaro ita kuma gwamnati a bangarenta tana fadin tana bakin kokarinta. Wace shawara za ki bayar?

 

Maganar tsaro babu abinda za mu ce, sai dai a koma ga Allah, tabbas jami’an tsaro na kokari, itama gwamnati tana kokari amma dai su kara daga inda suke a yau. Na biyu mu kan mu iyaye muna da rawar takawa musamman ganin yadda makarantu ma ba su tsira ba, akwai bukatar mu kara sanya idanu a tafiyar da tarbiyar ‘yayan mu, sannan mu horar da su mu’amala da mutanen kirki kuma mu kara da addu’a.

Wannan matsalar tsaron a kullun yana zuwa ne da sabon salo, idan an dakile can nan kuma ya bude. Dole mu tashi tsaye da addu’o’i tare da sanya idanu akan jama’a ke tafiyar da harkokin yau da kullun a yankunan mu. Mu taimakawa jami’an tsaro da bayanai su kuma su ji tsoron Allah su daina fallasa masu ba su baya nan sirri, domin wannan abin na daga cikin abubuwan da ke razana jama’a koda sun baki-baki sai su yi shiru.

 

A karshe menene fatan ki ga mata ‘yan uwanki da kuma samun zaman lafiya a kasar na ta fuskar kawo karshen rashin tsaro?

 

Shugabannin su ji tsoron Allah, su daina tauye hakkin mata, koda tsakanin mata da miji ne balle a tafiyar da shugabanci. Na biyu ina fatar matakan da gwamnati ke bi a yanzu zai bada damar samar da maslaha da zai haifar mana zaman lafiya. Duk wani yunkuri na gwamnati muddin ba zaman lafiya ba, ba za ta iya cin ma nasara balle har jama’a su samu aminci a tsakanin su da zai kawo kasa cigaba.

Exit mobile version