Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Ya Kamata A Yaki Da Talauci Ta Hanyar Koyon Fasahohi

Published

on

Zhang Dehua wanda shekarunsa suka kai 39 da haihuwa ya zo daga birnin Yiyang dake lardin Hunan na kasar Sin. A lokacin kuruciyarsa, mahaifinsa ya rasu, kuma ya bar makaranta, ya fara aiki sakamakon talauci. Don haka, ya yi kokari sosai da fatan samun canji a rayuwarsa. A shekarar 2008, bisa goyon bayan manufofin da gwamnatin birnin Yiyang ta gabatar, Zhang Dehua ya koma garinsu don kafa kamfani.

Hoto na farko:
A cikin shekaru 10 da fita waje tare da yin aiki, Zhang Dehua ya fi begen irin abincin ganyen Meigan na musamman na garinsu. A halin yanzu, mutane suna shan aiki, amma ana iya daukar abincin musamman na garinsu cikin sauki, hakan ya sa ake iya cin abincin a duk lokacin da ake so.
Hoto na biyu:
Bayan da aka kafa sansanin sabbin kamfanonin da matasan Yiyang suka kafa, Zhang Dehua ya samu damar yin hadin gwiwa da kwalejin kimiyya da fasahar abinci ta jami’ar aikin noma ta lardin Hunan. A sakamakon hakan, masana sun ba da shawarwari kan ayyukan da aka gudanar, kana manufofin da gwamnatin birnin ta gabatar sun samar da gudummawa kan ayyukan kamfanin Zhang Dehua, ana sa ido da kuma ba da taimako ga kamfaninsa a fannonin fasahohin shuka kayan lambu, da samar da kayayyaki a fannoni daban daban.
Hoto na uku:
Zhang Dehua ya taimakawa manoma da dama dake yankin Ziyang na birnin Yiyang wajen aikin samar da kayayyaki bisa bukatun da ake da su da yanayin da ake ciki. A shekarar 2019, an cimma nasarar kawar da talauci a kauyen Fumin da na Bayi na lardin, domin an kyautata tsarin kafa kamfanoni, da kuma kara samun masu kafa kamfanoni kamar Zhang Dehua da suka koma garinsu don taimaka wajen yaki da talauci. Kamfanin Zhang Dehua ya taimakawa iyalai masu fama da talauci 1193 na birnin Yiyang. Bayan da ya kafa sabon kamfani a garin Anhua a watan Yuni, kamfaninsa zai kara taimakawa masu fama da talauci dake wurin wajen kara samar da amfanin gona da kuma samun kudin shiga. (Mai Fassarawa: Zainab Zhang)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: